CKVL-FM (Gidan Rediyo)
Appearance
CKVL-FM | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | Tashar Radio |
Ƙasa | Kanada |
Harshen amfani | Faransanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 8 ga Janairu, 2008 |
ckvl.fm |
CKVL-FM (FM 100,1 Radio LaSalle) gidan rediyo ne na al'umma da ke Montreal, Quebec, Kanada, yana watsa shirye-shirye a 100.1 MHz. La radio communautaire de Ville LaSalle, wata kungiya ce mai zaman kanta ta mallaki kuma take sarrafa tashar.[1]
Tashar ta farko tana hidimar gundumar Montreal na Lasalle, wanda kuma shine wurin dakunan shirye-shiryensu da watsawa. Yawancin shirye-shiryen tashar da Faransanci ne; duk da haka, tashar kuma tana da izinin yin amfani da Turanci.[2]
Tashar ta kasance memba na Association of Community Radio Broadcasters na Quebec.