Chuka Momah
Chuka Momah | |
---|---|
Rayuwa | |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Najeriya, Nsukka |
Sana'a | |
Sana'a | sports journalist (en) |
Chuka Momah ⓘ ɗan jarida ne kuma mai kula da harkokin wasanni na Najeriya, tsohon shugaban hukumar kwallon Tennis ta Najeriya ne da kuma kungiyar kwallon Tennis ta Afrika. A shekarar 2013, ya wallafa Sports Spectacular, wani littafi game da labarun wasanni da nazarin wasanni a Najeriya.[1]
Karatu da Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Momah ya halarci Kwalejin Gwamnati da ke Ibadan, ya kammala karatunsa a fannin ilmin ƙananun halittu-(Microbiology ) a Jami'ar Najeriya, ya kasance memba a ƙungiyar wasan kurket ta jami'ar da ta lashe gasar kurket a wasannin NUGA na 1974. [2]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan kammala karatunsa, Momah ya yi aiki a wasu kamfanoni masu zaman kansu, inda ya yi ritaya a shekarar 1985 tare da Hoechst. Ya yi aiki a matsayin mai bugawa da watsa shirye-shiryen sharhi a sashen wasanni. Ya kasance marubuci ga National Concord, tsakanin shekara ta 1982 zuwa 1985 kuma edita mai bayar da gudummawa a mujallar Newswatch.[3] Ya kasance ma'aikacin watsa shirye-shiryen Wasanni na gidan talabijin na gwamantin tarayya NTA, har wayau, ya gabatar da shirin Big Fights on of the Decades a NTA ɗin.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Odegbami, Segun (January 18, 2014). "Sports Spectacular - a special tribute to Chuka Momah". Daily Trust (Abuja). Archived from the original on August 10, 2018. Retrieved August 9, 2018.
- ↑ "Momah: The Spectacular Super Fan - This Day News". www.nigeria70.com (in Turanci). Retrieved 2018-08-09.[permanent dead link]
- ↑ "MOMAH, Emmanuel Chuka". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). 2017-03-20. Retrieved 2018-08-09.