Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gyara.
Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gyara. | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gyara, wato CHRR, kungiya ce mai zaman kanta a kasar Malawi. An kafa kungiyar shekarar 1995, a matsayin kungiya mai zaman kanta, da ba ta da niyya, mai zaman kansa da aka yiwa rajista a karkashin Dokar Trustees Incorporation na 1962. Tsoffin dalibai da suka yi gudun hijira ne suka kafa kungiyar, wadanda suka koma gida ga alkawuran sabon dimokuradiyya a shekarar 1994.
An bawa kungiyar izinin samar da ayyukanta a ko'ina a Malawi. Rijistar ta a karkashin Dokar Haɗin gwiwa ta 1962, ta ba da tushen da ke bayyana aikin kungiyar da kuma girman aikin. Kungiyar tana gudanar da shirye-shirye a duk yankuna ukun wato; Kudancin, Tsakiya da Arewa.
CHRR tana neman ta ba da gudummawa ga aiwatar da wannan manufa ta hanyar shirye-shirye da yawa da aka gudanar ta hanyar manyan shirye-shiryen guda biyu wato: Ƙaddamar da Ƙarfafawa da Kula da Hakkin Dan Adam da Horarwa.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Bayanai masu zuwa sun fito ne daga bakin darektan CHRR Undule Mwakasungura sai dai idan an samu wasu bayanan da suka ci karo da wannan;[1]
An kirkiri Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gyara, wato CHRR a cikin shakarar 1994. Dalibai da aka kora ne suka kafa kungiyar wanda suka bar kasar a shekarun 1970s da 1980s. Sun fara ayyuka a wasu kasashen a matsayin 'yan kasuwa da sauran sana'oi. Sun dawo a shekara ta 1994 kafin fara zaben jam'iyyu daban daban. Kungiyar ta yi amfani da kwarewarta da iliminta a wajen bunkasa kariyar hakkin dan Adam. Mamban kungiyar na karshe da ya rage shine shugaban kungiyar na yanzu Undule Mwakasungura.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Undule Mwakasungura, Feb 2, 2008