Cin-zarafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Cin-zarafi
subclass ofhuman behaviour, social issue Gyara

Cin-zarafi ya tattara abubuwa da dama na ɗabi'u dake nuna kakkausar hali. Za'a iya fahimtar cewa ɗabi'a ce dake ƙokarin ƙasƙantar, da wulaƙantar ko kunyatar da wani mutum, kuma baya daga cikin dabi'u na al'umma da tarbiyu na hankali ko mutanen kirki. A fanni na shari'a, dabi'u ne da suke masu ƙuntatawa, tada rikici ko illitarwa. Suna somawa ne daga wuraren wariya, da kuma hana ko tunkuɗe mutum daga amfana da Yancin sa na yan'adam.

Ire-ire[gyara sashe | Gyara masomin]

Ubangida[gyara sashe | Gyara masomin]

Cin-zarafi na Ubangida na faruwa ne daga Ubangida ko mutumin dake wakiltar sa a wurin mazauna gidansa ko masu aiki a ƙarƙashin shi, a yanayi marasa daɗi ga Yan'hayansa saboda su bar masu gidan da suke haya a gunsu.

Yanar gizo[gyara sashe | Gyara masomin]

wuraren da ake yaɗa cin-zarafi[1] waɗanda matasa ke amfani da su a Amurka, a binciken Sashen kare cututtukar ƙasar[2]

Cin-zarafi kan nuna yawan maimaita obscenities da maganganun kaskanci ga wasu alumma da ake niyya, misali, akan addini, jinsi, ƙasa, rauni (nakasa), ko yanayin su. Cinzarafi irin wannan na faruwa ne a ɗakunan hira, ko gidajen cin abinci, majalisi, ko yaɗa zancen tsana ga wasu. Wanda ya had a da sace hoton wadanda akeson cinzarafin su, da musanya su zuwa ɓatanci, sannan a sake yaɗa su zuwa social media da burin ya haifar rashin kwanciyar hankali.

Yan'sanda[gyara sashe | Gyara masomin]

Mu'amalantar da jami'an tsaro keyi ga wasu, wanda ya hada da amfani da karfin iko da wuce kima, ban-banci wurin yin adalci, tsoratarwa, kabilanci, addini, jinsi, fyade, shekaru ko kuma wasu nau'ikan wariya.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Hertz, M. F.; David-Ferdon, C. (2008). Electronic Media and Youth Violence: A CDC Issue Brief for Educators and Caregivers. Atlanta (GA): Centers for Disease Control. p. 9.  Unknown parameter |access-date= ignored (help)
  2. Ybarra, Michele L.; Diener-West, Marie; Leaf, Philip J. (December 2007). "Examining the overlap in internet harassment and school bullying: implications for school intervention". Journal of Adolescent Health 41 (6 Suppl 1): S42–S50. PMID 18047944. doi:10.1016/j.jadohealth.2007.09.004. 
Wannan ƙasida guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.