Jump to content

City Of Bastards (Fim)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
City Of Bastards

City Of Bastards ya kasance fim ne mai ban sha'awa na kasar Najeriya, wanda akayi a shekara ta 2019, kuma Titilope Orire ya shirya sai Yemi Morafa ne ya ba da umarni a ƙarƙashin shirin samar da Studio na A Silueta Entertainment Studio. Fim ɗin da ke bayyana rayuwar yau da kullun na mutanen da ke cikin ƴan tauraruwar talakawa Ifu Ennada, Femi Branch Bolanle Ninolowo, Linda Osifo da Stan Nze.[1][2][3]

Fim din ya mayar da hankali ne kan jigogi daban-daban da suka shafi rayuwar jama'a musamman a yankunan karkara kamar tashin hankali tsakanin al'umma, shaye-shayen miyagun kwayoyi, karuwanci da fataucin yara. An ba da labarin fim ɗin tare da jarumi mai suna Sarki, wanda ke ƙoƙarin daidaita abubuwan da ya faru a baya da na yanzu don ya ci gaba da riƙe matsayinsa na Sarkin Talakawa.[3][1]