Cyril Godwin Hart
Cyril Godwin Hart | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Cyril Godwin Hart (an haife shi 25 ga watan Afrilu 1978) ɗan siyasan Najeriya ne kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Degema/Bonny na jihar Rivers a majalisar wakilai ta tarayya ( Nijeriya ). [1]
Rayuwar farko, ilimi da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Hart a ranar 25 ga watan Afrilu 1978. Ya yi digirin farko a fannin Injiniyanci na abinci daga Jami’ar Uyo, sannan ya zama tsohon Kwamishinan Hukumar, Hukumar Ilimi ta bai ɗaya ta Jihar Ribas.
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Hart ya fara harkar siyasa ne a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Bonny Island ta jihar Ribas a Najeriya kuma a watan Mayun 2022 ya fito a matsayin ɗan takara mai wakiltar Degema/Bonny Island a majalisar wakilan Najeriya ta PDP a jihar Ribas. Daga ƙarshe ya lashe zaɓen kuma aka rantsar dashi a watan Yuni 2023. [2]
A zaman da aka yi, Hart ya fice daga zaman, inda ya zargi mataimakin shugaban majalisar da nuna wariya ga sabbin ‘yan majalisar yayin muhawarar majalisar. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Majeed, Bakare (2 July 2024). "Lawmaker accuses deputy speaker of bias, stages walkout". Premium Times. Retrieved 30 July 2024.
- ↑ Tide, The (23 May 2022). "PDP Assembly, Reps Candidates Emerge In Rivers". :::...The Tide News Online:::... Retrieved 30 July 2024.
- ↑ Yakubu, Dirisu (2 July 2024). "Rep stages walkout, accuses deputy speaker of discrimination". Punch Newspapers. Retrieved 30 July 2024.