Daular Qajar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Daular Qajar
دولت علیّه ایران (fa)

Take First Iranian national anthem (en) Fassara

Wuri
Map
 35°42′00″N 51°25′00″E / 35.7°N 51.4166669°E / 35.7; 51.4166669

Babban birni Tehran
Yawan mutane
Harshen gwamnati Farisawa
Azerbaijani (en) Fassara
Addini Shi'a
Bayanan tarihi
Mabiyi Daular Afsharid
Ƙirƙira 1785
Rushewa 1925
Ta biyo baya Pahlavi Iran (en) Fassara
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati absolute monarchy (en) Fassara da constitutional monarchy (en) Fassara
Ikonomi
Kuɗi Iranian toman (en) Fassara

Qajar Iran (Farisawa ايران قاجارى Irân Qājāri) ana kuma kiranta da Qajar Farisa[1] (Farisawa فارس قاجارى Faris Qājāri), Daular Qajar (Farisawa شاهنشاهى قاجار Šāhanšāhi-ye Qājār), bisa hukuma Maɗaukakin Ƙasar Farisa (Farisawa دولت عَلیّهٔ ایران Dowlat-e 'Aliyye-ye Irân) kuma ana kiranta da Guarded Domains na Iran (Farisawa ممالک محروسهٔ ایران Mamâlek-e Mahruse-ye Irân[2]) kasa ce ta Iran[3] wacce daular Qajar ta mulki daga 1789 zuwa 1925. Iyalan Qajar sun mamaye Iran gaba daya a shekara ta 1794, inda suka kori Lotf 'Ali Khan, Shah na karshe na daular Zand kuma suka sake tabbatar da ikon Iran akan manyan sassan Caucasus. A cikin 1796, Agha Mohammad Khan Qajar ya ƙwace Mashhad cikin sauƙi,[4] wanda ya kawo ƙarshen daular Afsharid. Iran ta hade kuma aka ayyana Agha Muhammad Khan Qajar shah na daular.[5]

Daga baya juyin juya halin tsarin mulki ya faru. Bayan juyin mulkin da aka yi a zamanin mulkin Muzaffar al-Din Shah, sarki mai jiran gado Muhammad Ali Shah ya yi adawa da shi tare da rufe majalisar. Rikicin cikin gida da waje ya haifar da tashin hankali a kasar, kuma sarkin Qajar na karshe shi ne Ahmad Shah Qajar wanda aka hambarar da shi a shekara ta 1925 kuma Reza Pahlavi ya zama Shah na Iran.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Qajar Persia.
  2. History of Persia.
  3. Abbas Amanat, The Pivot of the Universe: Nasir Al-Din Shah Qajar and the Iranian Monarchy, 1831–1896, I. B. Tauris, pp 2–3
  4. H. Scheel; Jaschke, Gerhard; H. Braun; Spuler, Bertold; T. Koszinowski; Bagley, Frank (1981).
  5. Iran : History.
  6. Qajar.