Jump to content

Denis Nzioka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Denis Nzioka
Rayuwa
Haihuwa Nairobi, 6 ga Augusta, 1985 (38 shekaru)
ƙasa Afirka ta kudu
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan jarida

 

Denis Nzioka (an haife shi ranar 6 ga watan Augustan shekarar 1985). ɗan gwagwarmayar jima'i ne, mai fafutukar kare hakkin tsirarun jinsi tare da mai da hankali na musamman akan LGBTIQ da al'ummomin Ma'aikatan Jima'i a kasar Kenya da Afirka. Ya ba da gudummawa wajen samar da ƙungiyoyi da yawa da suka mayar da hankali kan haƙƙin yan luwadi/madugo da kuma karuwai yayin da yake tallafawa ƙungiyoyin yankin game da wanzuwar jima'i, cin gashin kai na jiki da zaɓe-bayyana.[1]


Majagaba, yana gudanar da, duk da a ɓoye, amintaccen gida na farko a Kenya ga mutanen LGBTQ a 2009. A lokaci guda kuma shi ne dan Kenya na farko da ya fara fitowa fili a gidan talabijin na kasa. Tun daga wannan lokacin, kafofin watsa labaru daban-daban na duniya suka buga labarinsa da shafukansa. Ya kuma kasance yana gabatar da shirye-shiryen talabijin da rediyo akai-akai.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara mujalla ta farko - kuma ita kadai ce - LGBTI a Kenya, Identity Kenya, haka kuma ita ce ta farko a Nahiyar da ma duniya baki daya a shekarar 2014, da ta kaddamar da manhajar labarai ta LGBTIQ akan Google Stores. Ya haɗa littafin 'My Way, Your Way or the Rights Way' kuma ya buga shi a shekara ta 2019 littafin tarihin kawayen Kenya suna magana game da haƙƙin LGBTIQ mai suna "Rafiki Zetu", wato, na farko a Afirka kuma duniya!

Ya kafa Kamfanin labarai na Denis Nzioka News Agency and Service a cikin shekara ta 2010[2] a matsayin cibiyar watsa labarai ta farko da sabis na LGBTQI, aikin jima'i da kuma ƙawancen al'umma a Kenya. Yana aiki don canza ra'ayin jama'a da halayen zamantakewa ta hanyar ba da rahoto na asali da sharhin al'umma. Yana bayar da shawarwari da kayan albarkatu.

Nadi[gyara sashe | gyara masomin]

An nada shi a matsayin daya daga cikin manyan 'yan kafar Tweeters guda goma na Duniya akan Jima'i da Ci gaba, baya ga samun wasu yabo da kyaututtuka.[3] Ya sami lambar yabo ta Sauti ta 2016 don 'daidaitaccen rahoto game da batutuwan da suka shafi jima'i,' kuma don bikin cikarsu shekaru 10, lambar yabo ta Afirka ta Kudu Feathers Awards ta ba shi lambar yabo ta 2018 na Afirka. Ya sami lambar yabo ta Munir Mazrui Lifetime Achievement Award ta "Munir Mazrui Lifetime Achievement Award" wanda Defenders Coalition suka bashi a wajen taron EA Activist Award da akayi a Tanzania.

Bincike[gyara sashe | gyara masomin]

A halin yanzu, yana gudanar da aikin bincike na kansa mai suna "Waiter, umenyonga ugali: LGBTI Rights and Human Rights". Yana ƙoƙari ya amsa tambayar, 'Shin haƙƙin LGBTIQ suna cikin menu na ƙungiyoyin farar hula na Kenya?' Yana fatan ya binciki yadda - in har ma - ƙungiyoyin jama'a a Kenya ke haɗa haƙƙin 'yan tsiraru na jima'i da jinsi a cikin dabarun ba da shawarwari da shirye-shiryen sauya zamantakewa.

Ya bayyana, a cikin shekara ta 2020, Taskokin 'Yan luwadi da 'Yan madigo na Kenya, wanda aka yiwa lakabi da KumbuKumbu, buɗaɗɗen shafin yanar gizo, da wurin ajiyar kuɗi kyauta don bayanan tarihi da al'adun ƙungiyar LGBTIQ a Kenya daga tsakiyar 1800 zuwa yanzu.

Rayuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

Dan luwadi a bayyane, Denis Nzioka shima uba ne. Yana zaune a Nairobi, Kenya.

Takara[gyara sashe | gyara masomin]

Nzioka, wanda ya kasance ɗan luwaɗi, ɗan takarar shugaban ƙasar Kenya a 2013.[4]

Wallafe-wallafe a matsayin edita[gyara sashe | gyara masomin]

"Rafiki Zeru: Labarun LGBTIQ na Kenya, kamar yadda Allies suka fada" Nairobi, 2019 My Way, Your Way, or Rights Way. Nairobi: shirin labari, 2011.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Hakkokin LGBT a Kenya

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. DeBernardo, Francis; Editor (2012-10-02). "Catholic Brother Cited as Founder of Kenya's LGBT Community". New Ways Ministry. Retrieved 2021-01-30.
  2. "Welcoming two new members to the HIV Justice Network team". HIV Justice Network. Retrieved 2021-01-30.
  3. "Top 10 tweeters on sexuality and development". the Guardian. 2014-02-04. Retrieved 2021-01-30.
  4. "Kenyan Gay To Contest For President". 256news.com. 27 October 2011. Retrieved 19 July2012.