Denise (Houphouët-BoignyHouphouët-Boigny), wata Malama ce ta kasar Ivory Coast kuma jami'iyyar diflomasiyya a halin yanzu tana aiki a matsayin jakadiyar Cote d'Ivoire a (UNESCO). Ita likita ce a fannin kimiyya kuma farfesa a fannin sinadarai da ma'adinai. Ita mamba ce a Kwalejin Kimiyya, Fasaha, Al'adu na Afirka da ƴan Afirka na Cote d'Ivoire.[1]
Houphouët-Boigny ta sami DUES-PC2 a cikin shekarar 1972 kuma ta sami digiri na biyu a Chemistry a shekara ta 1974 kafin ta sami DES a kimiyyar jiki (Physical science) a shekarar 1976 da digiri na uku a kimiyyar jiki (physical science) a shekara ta 1984.
Ta fara aikinta na koyarwa a Makarantar Ayyukan Jama'a ta ƙasa a Abidjan daga shekarun 1975 zuwa 1977 sannan ta koma Laboratory of Inorganic Materials Chemistry na UFR Satière Structural Sciences and Technologies a matsayin malama mai bincike.[2] Ta kasance mataimakiyar farfesa a Jami'ar Cocody a Côte d'Ivoire daga shekarun 1985 zuwa 1993 lokacin da ta zama cikakkiyar farfesa. ta kasance memba na Majalisar Kimiyya na Faculty of Sciences da Techniques 1993 daga shekarun 1996 kafin a naɗa ta a matsayin Daraktar Ilimi mai zurfi a Ma'aikatar Ilimi ta Cote d'Ivoire daga shekarun 1996 zuwa 2006.[3][4] ] An naɗa ta ta Dindindin Delegate na Jamhuriyar Cote d'Ivoire zuwa UNESCO tun a shekarar 2011 kuma ta zama memba a Ofishin Babban Taron UNESCO tun a shekarar 2019.[5][6]