UNESCO
UNESCO Hukuma ce mai kula da guraren tarihi na al'adu ta duniya, Majalisar dinkin duniya ce ta samar da ita. Hukumar ta UNESCO ce ke zabar waje tare da kulawa da shi. Wuraren sun hada da (dazuka, tsaunuka, tafkuna, Sahara, Gine gine da birane). Yazuwa shekarar 2014, akwai kuma irin wadannan wuraren guda 1007 a kasashe 161. Akwai wurare na al'adu 779 da wurare na min indallah 197 da kuma gine gine na haɗakar kafarori 31. Italiya ce tafi kowacce kasa yawan wadannan wuraren inda take da guda 50. UNESCO na bukatar kowanne dan'adam da ya taimake ta wajen kare wadannan wurare. Wasu lokutan UNESCO na biyan wani kasafi na kudade domin ganin anci gaba da kare hadi da taskance su wadannan wuraren. Kungiyar dake fafutukar kafa daular musulunci a yankin Iraki wati ISIS ta lalata wadannan wuraren da dama a kasashen Siriya da Iraki.
Wuraren
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu daga wuraren tarihi wanda hukimar UNICEF take taskance da su.
-
Persepolis, Iran
-
Wajen tarihi na Florence a kasar Italiya
-
Gunkin Yanci dake Amurika
-
Uluṟu-Kata Tjuṯa (Australiya)
-
Chichen Itza a Yucatán (Mexico)
-
Waje mai yarihi n St. Petersburg a (Rasha)
-
Gine gine na mutanen da dakuma tsaunin Wudang a (China)
-
Wajen shakatawa a (Kenya)
-
Kirama ta Zambezi a Afrika
-
Ginin Taj Mahal
-
Memphis da tsaunukan Guza a kasar Misira