Jump to content

Taj Mahal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Taj Mahal
ताज महल
تاج مَحَل
تاج محل
 UNESCO World Heritage Site
Wuri
ƘasaIndiya
Jihar IndiyaUttar Pradesh
Division of Uttar Pradesh (en) FassaraAgra division (en) Fassara
District of India (en) FassaraAgra district (en) Fassara
BirniAgra
Coordinates 27°10′30″N 78°02′31″E / 27.175°N 78.0419°E / 27.175; 78.0419
Map
History and use
Ginawa1631 - 1653
Shugaba Shah Jahan (1632)
Suna saboda Mumtaz Mahal
Addini Musulunci
Karatun Gine-gine
Zanen gini Ahmad Lahori (en) Fassara
Material(s) marble (en) Fassara
Style (en) Fassara Islamic architecture (en) Fassara
architecture of Iran (en) Fassara
Mughal architecture (en) Fassara
Tsawo 73 m
Yawan fili 17 ha
Muhimman Guraren Tarihi na Duniya
Criterion (i) (en) Fassara
Reference 252
Region[upper-roman 1] Asia and Oceania
Registration )
Visitors per year (en) Fassara 6,532,366
Offical website
  1. According to the UNESCO classification
kwalliyar katangar

Ginin Taj Mahal ma'ana "Tambarin Waje", wani sanannen wajen yawon ɓude ido ne a ƙasar Indiya wanda yake a birnin Agra wato kudu da bakin gabar kogin Yamuna na kasar Indiya. Daular Mughal ta sarki Shah jahan ce ta fara gina shi a shekara 1632, saboda da tunawa da abarkaunar sa wato matarsa Mumtaz Mahal. Ginin anyishi ne da tsawon murabba'in hekta 17 (ginin mai baya daya kunshi gine gine masu yawa kamar Masallaci da masukin baki da manyan dakunan kwana masu yawa.

An kammala ginin Taj Mahal ne bakidaya a shekarar 1643 to amma an cigaba da aiwatar da wasu bangarori na ginin har ya zuwa karin shekaru 10. Anyi amannar cewa ginin na Taj Mahal an kammalashi ne bakidaya a shekarar 1652 akan adadin kidin da yakai Rupee na kasar Indiya na lokacin miliyar 32 wanda aka kiyasta da darajar Rupee na kasar Indiya na yanzu daidai da Rupee biliyan 52.8 (daidai da dalar Amurika $miliyan 827). Masu zanen gini guda 20,000 ne suka gwada basirar su ta zana ginin karkashin jagorancin babban mai zane wato Ustad Ahmad Lahauri.

Hukumar dake kula da muhimman wuraren tarihi ta majalisar dinkin duniya wato UNESCO World Heritage Sites ta saka Taj Mahal cikin jerin ta tare da yi masa lakabi da Jagoran zanen gini na Musuluci a kasar indiya tare kuma da saka shi a matsayin daya daga cikin abubuwan al'ajabi aduniya wanda dan adam ya hada. Akan samu masu ziyara Taj Mahal domin yawon bude ido kamar miliyan 7-8 a kowacce shekara.

Tsari da zana gini

[gyara sashe | gyara masomin]
wani nau,i na ginin Taj Mahal

Tsarin ginin Taj Mahal yana nuna irun tsarin gine gine ne na mutanen Parisa da kuma na tsohuwar daular Mughal da akayi a baya.

Hasumayar ginin itace tsakiyar ginin Taj Mahal. Wani babban farin hasumaya ce mai ado da zane zane mai daukar hankali.