Diassonema Mucungui
Diassonema Mucungui | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 6 ga Yuni, 1996 (28 shekaru) |
ƙasa | Angola |
Karatu | |
Harsuna | Portuguese language |
Sana'a | |
Sana'a | judoka (en) |
Mahalarcin
|
Diassonema Mucungui (an haife ta ranar 6 ga watan Yunin 1996)[1] 'yar wasan Judoka ce ta kasar Angola. Ita ce ta samu lambar tagulla a gasar wasannin Afirka kuma ta samu lambar yabo sau uku a gasar Judo ta Afirka. Ta wakilci Angola a gasar bazara ta shekarar 2020 da aka gudanar a Tokyo, Japan. [2]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2019, ta ci daya daga cikin lambobin tagulla a gasar mata ta kilogiram 57 a gasar Judo ta Afirka da aka gudanar a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.[3][4] A shekarar 2020, ta lashe lambar zinare a wannan gasar a gasar Judo ta Afirka da aka gudanar a Antananarivo, Madagascar.[5] [6]
Ta fafata a gasar tseren kilogiram 57 na mata a gasar Judo World Masters na shekarar 2021 da aka gudanar a Doha, Qatar. [7] Ta kuma yi gasar tseren kilogiram 57 na mata a gasar bazara ta shekarar 2020 da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan.
Nasarorin da aka samu
[gyara sashe | gyara masomin]Shekara | Gasar | Wuri | Ajin nauyi |
---|---|---|---|
2017 | Gasar Cin Kofin Afirka | 3rd | -57 kg |
2019 | Gasar Cin Kofin Afirka | 3rd | -57 kg |
2019 | Wasannin Afirka | 3rd | -57 kg |
2020 | Gasar Cin Kofin Afirka | 1st | -57 kg |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Diassonema Mucungui" . JudoInside.com . Archived from the original on 2017-09-16. Retrieved 19 December 2020.
- ↑ "Judo Results Book" (PDF). 2020 Summer Olympics . Archived (PDF) from the original on 1 August 2021. Retrieved 1 August 2021.Empty citation (help)
- ↑ Etchells, Daniel (25 April 2019). "Home favourite Whitebooi strikes gold on opening day of African Senior Judo Championships" . InsideTheGames.biz . Retrieved 27 December 2020.
- ↑ "2019 African Judo Championships" . African Judo Union . Archived from the original on 4 September 2019. Retrieved 20 August 2020.
- ↑ Pavitt, Michael (17 December 2020). "Whitebooi retains title as African Judo Championships begins in Madagascar" . InsideTheGames.biz . Retrieved 5 July 2021.
- ↑ "2020 African Judo Championships" . African Judo Union . Archived from the original on 26 December 2020. Retrieved 26 December 2020.
- ↑ "2021 Judo World Masters" . International Judo Federation . Archived from the original on 2021-01-12. Retrieved 12 January 2021.