Jump to content

Dibiagwu Eugene Okechukwu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dibiagwu Eugene Okechukwu
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Dibiagwu Eugene Okechukwu ɗan siyasan Najeriya ne. A yanzu haka mamba ne mai wakiltar mazaɓar Ohaji/Egbema/Oguta/Oru ta Yamma a majalisar wakilai. [1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Dibiagwu Eugene Okechukwu a ranar 24 ga watan Disamba 1971. [2]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Eugene dai ya gaji Uju Kingsley Chima ne bayan ya tsaya takara a zaɓen ‘yan majalisar wakilai na shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC kuma ya samu nasara inda ya doke takwarorinsa na jam’iyyun adawa. [3] [1] A wani ɓangare na tallafi da karfafawa, ya raba wa manoman mazaɓar sa iri na shuka don ƙara yawan abinci. [4]

Ƙalubale na shari'a da nasara

[gyara sashe | gyara masomin]

Kotun sauraren kararrakin zaɓe ta jihar Imo da ke zamanta a jihar Nasarawa ta tabbatar da nasarar Eugene Okechukwu a zaɓen shekarar 2023, inda daga karshe ta yi watsi da ƙarar da abokin takararsa Ilo Ezenwa Collins na jam'iyyar Labour (LP) ya shigar bisa dalilin cewa ba ta cancanta ba. . [5]

  1. 1.0 1.1 ""You All Will Be Proud That You Hired Me As Your Reps. Member", Hon Dibiagwu Assure Constituents". www.thenigerianvoice.com. Retrieved 2024-12-14. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. "10th National Assembly Members - Voter - Validating the Office of the Electorate on Representation". orderpaper.ng. Retrieved 2024-12-14.
  3. "2023 Imo state house of representatives election results - eduweb" (in Turanci). Retrieved 2024-12-16.
  4. "Food Production: Dibiagwu Empowers 150 Constituents With Improved Agricultural Seedlings". Pressman. 29 July 2023. Retrieved 16 December 2024.
  5. Tsa, Godwin (7 September 2023). "Imo House of Reps seat: Tribunal declares Dibiagwu Okechukwu winner". The Sun Nigeria. Retrieved 16 December 2024.