Dorcas Idowu
Appearance
Dorcas Idowu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 27 ga Augusta, 1903 (121 shekaru) |
ƙasa | Kameru |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Kamerun National Congress |
Dorcas Ewokolo Idowu (an haife ta 27 ga Agusta 1903) yar siyasar Kamaru ce. Ita ce mace ta farko da ta fara zama a Majalisar Dokokin Kudancin Kamaru,kuma 'yar majalisa ta farko a kasar Kamaru.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Idowu a shekarar 1903,diyar Joseph Lifanjo Ekema.[1] Ta auri Thomas Faguma Idowu kuma ta yi aiki a matsayin malami a makarantar gwamnati da ke Buea.[1] [2]
Wani memba na Kamerun National Congress,[2] An nada Idowu a Majalisar Wakilan Kudancin Kamaru a watan Yuli 1955 a matsayin memba mai wakiltar muradun mata,[1] ta zama 'yar majalisa ta farko a Kamaru.[2] Ta kasance memba har zuwa 1959.[3]