Doro
Doro ya kasance gari ne har da hakimi, me gudanar kansa a fadan Sarkin katsina. Garin na ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bindawa[1].
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Masana tarihi sun nuna cewa Doro ya samo asalin sunansa ne daga sunan wata mata da ake kira “A’i Mai Ɗan Doro”.[2] Ana tsammani matan tayi hijira daga garin shuni wanda ke cikin garin jihar sakkwato a ƙaramar hukumar Shuni,tare da ɗan uwanta Mani da jama’arsu. Sun fara sauka a inda Mani yake yanzu, daga baya suka tashi suka matsa zuwa inda Doro take a yau. Ance A’i Mai Ɗan Doro ta samu matsala da ƙaninta watau Mani sai ta koreshi ya koma garin da suka baro watau Mani, ita kuma ta tsaya ta kafa ɗan gari me suna“Doroyal” wanda ke kusa da Doro ta yanzu, daga wannan suna na A’i Mai Ɗan Doro aka sami “Doro” da kuma sunan sarautar garin “Ɗan Doro[1]”.
Ba a samu bayani ba game da mazaunan farko ba sai de tarihi ya nuna cewa Haɓe da Fulani ne mafi yawan Mazaunan Doro, sannan an nuna garin ya kai shekara Dubu da kafuwa[1]. Sannan ga dukkan alama akwai mutane a garin kafin zuwan A’i da mutanenta. Daga baya wasu shahararrun mutane sun ƙara zuwa daga garin Sakkwato suka sake kafa unguwannin Doro, mutanen Doro:
- Jibrin wanda ya kafa unguwar ƙetare
- Ibrahim Diro ya kafa unguwar ƙofar Arewa (Dajal)
- Mallam Maude Ya kafa ƙofar gabas
- Mallam Zango ya kafa ƙofar Zango[3].
Shuwagabannin Doro
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu daga cikin shuwagabannin Doro sun haɗa da:
- Ɗan Doro Habibu
- Ɗan Doro Gagaru Ɗan Habibu
- Ɗan Doro Dutsanya (daga,mani,ba fulatani ne)
- Ɗan Doro Nuhu (kankiya Nuhu)
- Ɗan Doro Bawa (daga tuwaru, fulani ne)
- Ɗan Doro Ibrahim (daga sarkin dikko, ƙanin dikko ya haife shi)
- Ɗan Doro Abubakar Ɗan Ibrahim[1].
Garin Doro yana da ganuwa da kuma rijiyoyi guda casa’in da tara anda wani ɗan ƙaruna da mutanensa suka gina a rana ɗaya kuma har yanzu ana shan ruwa daga garesu[4].
A fannin tattalin arziƙki kuwa, mutanen Doro sun shahara kan noma da kiwo daa saƙa da rini da sassaƙa. Kuma akwai ƴan kasuwa, da masu sufiri dakuma ƴan boko a garin Doro. A fannin cigaba kuma an gina asibitin shan magani kyauta da kuma makarantun firimari[4].
Camfi (Doro)
[gyara sashe | gyara masomin]Daga cikin abubuwan ban mamaki na garin Doro shine, Har yanzu babu maƙera a Doro sai dai ƙauyenta, wai saboda ance duk wanda yayi kira zai mutu. Sannan kuma duk wanda Ɗan Doron da aka naɗa dole ya shigo ta ƙofar kudu, idan ba haka ba zai haukace. Haka kuma idan an ɗauko amarya dole ta ƙofar kudu za abiyo da ita idan ba haka ba zata haukace[5].sun chanfa abubuwan.
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.31 ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.31 ISBN 978-2105-93-
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. pp. 30-31 ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 4.0 4.1 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. pp. 31-32. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 32 ISBN 978-2105-93-7.