Duwatsun Sankwala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Duwatsun Sankwala
General information
Height above mean sea level (en) Fassara 1,800 m
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 6°32′N 9°16′E / 6.53°N 9.27°E / 6.53; 9.27
Kasa Najeriya

Duwatsun Sankwala tsaunuka ne da ke a ƙaramar hukumar Obanliku ta Jihar Cross River a Najeriya. Duwatsun Sankwala na kudu maso gabashin garin Obudu, arewacin sashin Okwangwo na wurin shakatawa na ƙasa, na Jihar Cross River. Duwatsun sun kai tsawon kimanin 1,800 metres (5,906 ft).[1]

Yanayi[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai yanayin sanyi a wurin Duwatsun Sankwala. Hakan ya ja hankalin masu yawon buɗe ido zuwa wurin a cikin 'yan shekarun nan zuwa Obudu Plateau akan Dutsen Sankwala. [2]

Ayyukan yawon bude ido[gyara sashe | gyara masomin]

Ana samun alkaluman masu yawa na masu zuwa yawon buɗe idanun a Duwatsun Sankwala a kowace shekara. Wannan ya haifar da ci gaban Duwatsun Obudu a ɗaya daga cikin tsaunuka na wurin, wanda aka sani da sunan Oshie Ridge.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Oates, John F. (2004). Advances in Applied Biodiversity Science: Africa's Gulf of Guinea Forests: Biodiversity Patterns and Conservation Priorities. 6. doi:10.1896/1-881173-82-8. ISBN 1-881173-82-8.
  2. http://www.come2africa.net/westafrica/nigeria/destinations/obudu-mountain-resort.html[permanent dead link]
  3. "Obudu Mountain Resort, Nigeria's best kept secret". www.naijanewsandevents.com. Archived from the original on 4 September 2012. Retrieved 6 June 2022.