Edward John Eyre High School
Edward John Eyre High School | ||||
---|---|---|---|---|
makarantar sakandare | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 1968 | |||
Ƙasa | Asturaliya | |||
Authority (en) | Department for Education (en) | |||
Lambar aika saƙo | 5608 | |||
Shafin yanar gizo | ejehs.sa.edu.au | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Asturaliya | |||
State of Australia (en) | South Australia (en) |
Makarantar Sakandare ta Edward John Eyre tana cikin Whyalla Norrie, South Australia. An buɗe makarantar a shekarar alif ɗari tara da sittin da takwas 1968 a matsayin Eyre Technical High School.[1]
An gina makarantar a lokacin bunƙasa, yawan rajistar ɗalibai ya kai kusan 1,500 a cikin shekarar alif ɗari tara da saba'in 1970[1]. A yau, Makarantar Sakandare ta Edward John Eyre, wacce kuma akafii sani da Babban Makarantar Sakandare ta Whyalla, tana da yawan ɗalibai sama da ɗari huɗu 400.[2]
Makarantar Sakandare ta Eyre tana kula da ɗimbin ɓangarori na al'umma. Shirin Mum na Matasa yana tallafawa iyaye mata don kammala karatunsu.[2] Shirin Pre-Industry da Makarantar Ciniki yana taimaka wa ɗalibai a shirye-shiryen a cikin wuraren kasuwanci. Kwas ɗin wasan ƙwallon ƙafa na ƙwararrun yana haifar da nasara a cikin jiha da gasa na ƙasa.
Edward John Eyre High an ba da shawarar haɗa shi da Makarantar Sakandare ta Whyalla da Makarantar Sakandare ta Stuart. Sabuwar makarantar da aka haɗa ana nufin ta kasance akan titin Nicolson, Whyalla Norrie tsakanin cibiyoyin Whyalla na Jami'ar South Australia da TAFE SA kuma ana sa ran buɗewa don shekarar makaranta ta 2022.[3]