Eli Mwanang'onze

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Eli Mwanang'onze
Member of the National Assembly of Zambia (en) Fassara

Rayuwa
ƙasa Zambiya
Karatu
Makaranta University of Manitoba (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Malami
Imani
Jam'iyar siyasa United National Independence Party (en) Fassara

Dr Elimelek Hanakumbo Bulowa Mwanang'onze kwararren Malami ne a fannin ilimi ɗan ƙasar Zambia kuma tsohon ɗan siyasa. Ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Dokoki ta ƙasa mai wakiltar Bweengwa daga shekarun 1988 har zuwa 1991,[1] da kuma riƙe muƙamin Ministan Ilimi, Matasa da Wasanni. [2]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Mwanang'onze ya sami MSc a fannin ilimin ƙasa a Jami'ar Manitoba a shekara ta 1974, kafin ya sami digiri na uku a jami'a guda a shekarar 1978. Daga baya ya yi aiki a matsayin malami a Makarantar Mines a Jami'ar Zambiya, [3] kuma ya kasance shugaban kwamitin edita na Journal of African Marxists. [4] Daga baya ya zama ma'aikacin gwamnati kuma ya kasance babban sakataren ma'adinai. [5]

An zaɓi Mwanang'onze a matsayin ɗan majalisar dokokin ƙasar ne a babban zaɓen ƙasar na shekarar 1988 a daidai lokacin da ƙasar Zambiya ta kasance ƙasa mai jam'iyya ɗaya da jam'iyyar 'yancin kai ta United National Independence Party a matsayin jam'iyyar doka tilo.[6] Lokacin da aka ɓullo da tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da yawa a farkon shekarun 1990, bai tsaya takara a babban zaɓen shekara ta 1991 ba kuma Baldwin Nkumbula ya gaje shi. [7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Debates- Friday, 21st October, 2011". National Assembly of Zambia. Retrieved 9 February 2020.
  2. World Conference on Education for All UNESCO
  3. Yong Zhou (2013) The Development Potential of Precambrian Mineral Deposits: Natural Resources and Energy Division, U.N. Department of Technical Co-Operation for Development, Elsevier, p427
  4. Journal of African Marxists Ufahamu: A Journal of African Studies
  5. "Low copper prices threaten nation's mining future", Times of Zambia, 9 September 1982
  6. Yong Zhou (2013) The Development Potential of Precambrian Mineral Deposits: Natural Resources and Energy Division, U.N. Department of Technical Co-Operation for Development, Elsevier, p427
  7. Zambia Election Passport