Elisabeth Tankeu
Appearance
|
| |||
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Yabassi (en) | ||
| ƙasa | Kameru | ||
| Mutuwa |
Neuilly-sur-Seine (mul) | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
Elisabeth Tankeu (29 Fabrairu 1944 – 16 Oktoba 2011) 'yar siyasar Kamaru ce. Ita ce kwamishiniyar ciniki da masana'antu ta Tarayyar Afirka.[1]
Aiki siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]
Daga shekarun 1976, zuwa 1979, Tankeu ta kasance mataimakiyar darakta mai kula da tsare-tsare na Kamaru sannan daga shekarun 1980 zuwa 1983, ta kasance Darakta a wannan ma'aikatar. Daga shekarun 1983, zuwa 1988, ta kasance mataimakiyar ministar tsare-tsare ta masana'antu sannan daga shekarun 1988 zuwa 1992, ministar tsare-tsare da raya yankuna.[2]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Tankeu ta mutu a ranar 16 ga watan Oktoba 2011, a wani asibiti a Paris, Faransa.[3] An binne ta ne a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2011, a Bangoua, garin mahaifar mijinta a yammacin Kamaru.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Countries in Africa plan tack for G-8 meeting". The New York Times. 5 July 2005. Retrieved 2009-10-20.
- ↑ "Countries in Africa plan tack for G-8 meeting". The New York Times. 5 July 2005. Retrieved 2009-10-20.
- ↑ "Cameroon mourns: Former Minister Elisabeth Tankeu dies in Paris". Cameroon Radio & Television. 18 October 2011. Archived from the original on 17 January 2012. Retrieved 20 October 2011.