Jump to content

Evans Chan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Evans Chan
Rayuwa
Haihuwa 20 century
Sana'a
Sana'a darakta
Fafutuka Hong Kong Second Wave (en) Fassara
IMDb nm0150886

Evans Chan (陳耀成) darektan fim ne na kungiyar Second Wave daga Hong Kong. Yawanci fina-finansa sunfi mayar da hankali ne kan nuna ainihin mutanen Hong Kong, kamar irinsu oo Liv (e) (1992), Crossings (1994), da kuma The Map of Sex and Love ( (2001).

To Liv(e) shine mafi shahara daga cikin ayyukansa. A ciki jarumar ta rubuta wasika zuwa ga fitacciyar kasar NorwayLiv Ullmann don nuna rashin jin dadin ta game da sukar da take yi kan manufofin gwamnatin Hong Kong da ke mu'amala da mutanen jirgin ruwan Vietnam. Fim din dai wani misali ne da ya shafi rikicin ainihin mutanen Hong Kong inda suke fuskantar zanga-zangar Tiananmen ta shekarar 1989 da kisan kiyashi da mika mulki a shekarar 1997.

To Liv (e) ya sami yabo sosai daga malaman ilimi da masu sukar fim. Fim din ya samu lashe lambobin yabo na 'yar wasan kwaikwayo ta musamman (Lindzay Chan) da kuma 'yar wasan ta biyu na musamman (Josephine Koo) a bikin fina-finai na Golden Horse na 1992.

Hotunan fina-finai

[gyara sashe | gyara masomin]

Haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]