Eze Ukwu
Eze Ukwu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Nnewi, 1799 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 15 ga Augusta, 1862 |
Ƴan uwa | |
Yara |
view
|
Sana'a |
Eze Ukwu (an haife shi 1799-1862) shine Obi na 15 na Otolo da Igwe na masarautar Nnewi.[1] Ya kasance babban basarake kuma shugaban ruhaniya a Nnewi, garin Igbo a Najeriya. Ya kasance dan kabilar Nnofo Royal kuma magajin mahaifinsa Eze Chukwu.[2] Ba kamar yawancin sarakunan Ibo ba, akwai sarakunan Nnewi kafin zuwan Turawa.[3]
Mulki
[gyara sashe | gyara masomin]A lokacin mulkinsa, abubuwa masu muhimmanci sun faru. Ya ki yarda da shawarar kawunsa, Eze Enwe, na kawo karshen yakin da aka yi da Amichis. Saboda haka Eze Enwe ya fara aikin. Ya mamaye Amichis kuma ya ci su, ya lashe wannan nasara tare da kama Nwamkpi, shugabansu tare da kashe shi. ya yi nasarar sake yin yaki da Ųkpo kuma ya shiga cikin nasarar mamaye Orifite.[4] Wadannan nasarori masu ban mamaki sun ba shi damar samun lakabin jaruntaka na "Onuo ora", wanda ya ba mutum damar mallakar Ikponasato, wato, (eight very small bells).[5]
Bayan okafo, dan farko na Eze Ukwu, yana da 'ya'ya masu zuwa kamar haka: - Eze Oruchalu da Unaegbu. Lokacin da Eze ukwu ya rasu, Igwe Okafo, babban dansa, ya zama sarki na goma sha shida.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Admin, Nnewi. "List of Nnewi Monarchs - The Official Nnewi City Portal". www.nnewi.info. Retrieved 2015-09-17.[permanent dead link]
- ↑ Onwutalobi, Anthony-Claret. "Nnofo Royal Lineage - The Official Nnewi City Portal". www.nnewi.info. Archived from the original on 2021-06-19. Retrieved 2015-09-17.
- ↑ Onwutalobi, Anthony-Claret. "Nnewi Monarchy - The Official Nnewi City Portal". www.nnewi.info. Archived from the original on 2021-06-23. Retrieved 2015-09-17.
- ↑ Onwutalobi, Anthony-Claret. "History - The Official Nnewi City Portal". www.nnewi.info. Archived from the original on 2015-11-10. Retrieved 2015-09-17.
- ↑ Alutu, Dr. John Okonkwo (1986). Nnewi History (from the Earliest times to 1980/82)29. Nigeria: Fourth Dimension Publishers. p. 29. ISBN 9781562242.