Fataucin mutane don karuwanci a Japan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fataucin mutane don karuwanci a Japan
sex trafficking by country or territory (en) Fassara
Bayanai
Bangare na human trafficking in Japan (en) Fassara
Ƙasa Japan

Fataucin abinda ya shafi Jima'i a Japan ana fataucin mutane ne da nufin yin lalata da bautar su a ƙasar japan. Japan ƙasa ce ta asali, wadda ake yawan ziyarta, haka kuma ƙasa ce da ake safarar ƴan'mata musamman masu ƙananan shekaru don maida su karuwai da yin lalata da su ba bisa son su ba.

Karfi da yaji[gyara sashe | gyara masomin]

Ƴan ƙasar Japan, musamman mata da ƴan'mata, ana yin safarar su ta hanyar maida su karuwai da ƙarfi da yaji a cikin Japan da kuma zuwa wasu ƙananan ƙasashen waje. Ana safarar waɗanda su ke daga ƙasashen waje zuwa cikin ƙasar japan. Yara, kanana, da mutanen da suka fito daga iyalai marasa ƙarfi wato waɗanda talauci ya musu katutu sun fi fuskantar matsalar fataucin jima'i/shiga cikin harkar karuwanci.Ana yaudarar waɗanda aka yi fataucin su don manufar karuwanci, [1] [2] ana yi musu barazana, [2] [3] [4] da tilasta musu yin karuwanci.Masu safarar mutane (waɗanda suka kama su) suna kwace fasfo ɗinsu da takardun banki da duk wasu muhimman takardun da suka shafe su. [2]Ana yawan ɗaura musu basussuka don su biya su fanshi kansu daga halin da suke ciki.[2] [3]Ana musu raunuka sosai saboda duka ta ko ina a jikin su shiyasa basu rabuwa da rauni a jikin su, haka ana musu barazanar kisa da kuma tada musu hankali.[4] [5]Da yawa daga cikin waɗanda akayi safarar su suna kamuwa da cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i da fyaɗe kuma suna rayuwa a cikin yanayi mara kyau rayuwar ƙunci da wahalhalu. Wasu waɗanda aka ceto suna fuskantar wariya, baƙin ciki,[5] wani lokacin har suna yunƙurin kashe kansu.[4]Akan ɗauke su hotuna a lokacin da suke tsirara sai a watsa hotuna a yanar gizo don muzanta su. [4]

Masu fataucin[gyara sashe | gyara masomin]

Masu fataucin maza da mata a Japan sun fito ne daga wurare dabam-dabam da kowane fanni na zamantakewa. Masu safarar mutane galibin su membobi ne da kuma ƙungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, suna haɗuwa ne su cure waje ɗaya don samun sauƙi wajen aikata miyagun Laifuka. sunada alaƙa da ƙungiyoyin yakuza ko boryokudan. An danganta fataucin jima'i da masana'antar nishaɗi da yawon buɗe ido ta Japan, kuma ana fataucin mata da 'yan mata zuwa kasuwancin da ke ba da hidimar soja da 'yan kwangila a cikin Sojojin Japan na Amurka. Masu fataucin mutane suna yin amfani da gidajen yanar gizo, irin su imel, da apps don yaudarar waɗanda abin ya shafa. Ƴan ƙasar Japan sun tsunduma cikin safarar jima'i ta yanar gizo.

Ciniki[gyara sashe | gyara masomin]

Girman cinikin jima'i a Japan yana da wuya a sani saboda yanayin yadda masu aikata laifukan ke ɓoye komai da ya shafi fataucin jima'i, kasancewar wasu tsiraru kaɗan ne kawai ake kai rahoto ga hukuma, da sauran dalilai.An soki gwamnatin Japan da rashin ƙoƙarinta na rashin yaƙi da safarar mutane da tilasta musu yin karuwanci a cikin dokokinta. Ana zargin wasu jami'an kasar Japan da nuna halin ko in kula game da lamarin.

`Yammta[gyara sashe | gyara masomin]

Galibi dai waɗanda abin yafi shafa sune `yanmamatane da suka fito daga gidajen marasa karfi. akan yaudaresu ne ta hanyar nuna masu za`a sama masu ayyukan yi acen, sai dai da ansamu nasarar kaisu kashehen sai lamari ya sh ban-ban.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named VOA 2017
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named The Mainichi 2017
  3. 3.0 3.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named UW–Madison News 2018
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named TIME 2019
  5. 5.0 5.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named The Washington Post 2017