Fatima Musa
Fatima Musa ta kasance jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood tana daya daga cikin kyawawan mata a masana'antar ta hausa, anfi kiranta da suna macijiya sakamakon fim din macijiya datayi ta fito a matsayin macijiya, shiyasa ake mata lakabi dashi.
Takaitaccen Tarihin ta
[gyara sashe | gyara masomin]Cikakken- sunan ta shine fatima Musa an haife ta a shekarar 1989, yar kabilar gbaygi wacce anan bangaren ake kira da gwari, masoyan ta suna Kiran ta da fati macijiya sakamakon fim din macijiya da tayi, tsohuwar jaruma ce a masana'antar kanniwud tana daya daga cikin kyawawan mata a masana'antar, Haifaaffiyar jihar niger ce garin nufawa, tayi karatun firamare da sakandiri har zuwa Jami,a a can , tana zaune da Yan uwanta da iyayen ta a jihar nija. Bayan ta gama karatu ne ta dawo cikin jihar Kano saboda ta zamo jaruma, tazo a sa,a domin da farawar ta ta shara ta daukaka[1][2]
Finafinai
[gyara sashe | gyara masomin]- macijiya
- Ranar juma,a
- Galaba
- Da kishiyar gida
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.
- ↑ http://hausafilms.tv/actress/fati_macijiya_musa