Fatma Moalla
Fatma Moalla | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tunis, 14 ga Janairu, 1939 (85 shekaru) |
ƙasa |
French protectorate of Tunisia (en) Tunisiya |
Karatu | |
Makaranta |
Pacha Street Lyceum (en) Carnot Lyceum of Tunis (en) Institut des Hautes Etudes de Tunis (en) |
Sana'a | |
Sana'a | masanin lissafi |
Kyaututtuka |
Fatma Moalla (an haife ta a ranar 14 ga watan watan Janairu 1939) ƙwararriya ce a fannin lissafi 'yar Tunisiya wacce ta wallafa bincike a kan Finsler spaces da lissafin geometry kuma ta yi aiki a matsayin mataimakiya a Faculté des Sciences Mathématique, Physiques et Naturelles. Yanzu haka an ba ta lambar yabo ta ƙasa da kasa Fatma Moalla don shaharar ta a ilimin lissafi don karrama ta (The International Fatma Moalla Award for the Popularization of Mathematics).[1]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Fatma Moalla a birnin Tunis na ƙasar Tunisia a ranar 14 ga watan Janairu, 1939. Sunan mahaifinta Mohamed Moalla kuma yana aikin sayar da littattafai. Ta halarci makarantar sakandare a Lycée de la Rue du Pacha. A cikin shekarar 1956, Moalla ta sauya makarantu kuma ta fara halartar Lycée Carnot ta Tunis inda ta zaɓi ta kware a fannin lissafi. Daga nan sai Moalla ta halarci jami'a a "Institut des Hautes Études de Tunis...[da] Ta kammala karatu tare da digirinta na lissafi a watan Yuni 1960."[1] Moalla ita ce 'yar Tunisiya na farko da aka ba ta lambar yabo a fannin lissafi a Faransa a shekarar 1961 kuma mace ta farko 'yar Tunisiya da ta samu digiri na uku a fannin lissafi a Faransa a shekarar 1965.[2] Daga baya aka sanya ta cikin kungiyar matan Tunisiya ta ƙasa.
Kyaututtuka da nasarori
[gyara sashe | gyara masomin]An bata lambar yabo ta Fatma Moalla na duniya don shaharar ta a ilimin lissafi a kowace shekara don girmamawa ga Fatma Moalla (The International Fatma Moalla Award for the Popularization of Mathematics).[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 O'Connor, John J.; Robertson, Edmund F., "Fatma Moalla", MacTutor History of Mathematics archive, University of St Andrews.
- ↑ "The International Fatma Moalla Award for the Popularization of Mathematics | African Women in Mathematics Association". 2019-07-15. Archived from the original on 2019-07-15. Retrieved 2019-07-15.
- ↑ "International Fatma Moalla Award | University of Tübingen". uni-tuebingen.de. Retrieved 2019-07-10.