Filin shakatawa na Lopé
Filin shakatawa na Lopé | ||||
---|---|---|---|---|
national park (en) | ||||
Bayanai | ||||
Bangare na | Ecosystem and Relict Cultural Landscape of Lopé-Okanda (en) | |||
Farawa | 2002 | |||
IUCN protected areas category (en) | unknown value | |||
Ƙasa | Gabon | |||
Ma'aikaci | National Agency for National Parks (en) | |||
Wuri | ||||
|
Filin shakatawa na Lopé shi ne wurin shakatawa na ƙasa a tsakiyar Gabon. Duk da cewa filin galibi dajin monsoon ne, a arewacin wurin shakatawa yana ɗauke da ragowar ciyawar savannas na ƙarshe da aka ƙirƙira a Afirka ta Tsakiya a lokacin Ice Age na ƙarshe, shekaru 15,000 da suka gabata. Shine yanki na farko da aka kiyaye shi a Gabon lokacin da aka kirkiri wurin ajiyar namun daji na Lopé-Okanda a shekarar 1946. A shekarar 2007, UNESCO ta kara shimfidar yankin Lopé-Okanda a cikin jerin kayayyakin tarihin duniya.
Gidan shakatawar na ɗauke da wata karamar tashar bincike, mai suna Mikongo kuma karkashin kulawar kungiyar kula da dabbobi ta London, wacce ke zaune a ƙauyen da ake kira Mikongo, wanda daga nan ne aka samo sunan. Akwai kayayyakin more rayuwa da za a iya kula da su ga masu yawon bude ido a gindin, gami da chalet da dama da kuma babban dakin cin abinci a sararin sama, wanda daga dajin da ke da nisan mil biyar ne kawai.[1] Har ila yau, wurin shakatawar na daukar bakuncin CEDAMM Training Centre, cibiyar kula da kare namun daji da ke kula da cibiyar ba da ilimi ta kiyayewa ta duniya.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "AP via Washington Post "UNESCO Committee Renames Auschwitz" 28 June 2007". Archived from the original on 2 November 2012. Retrieved 26 October 2017.