Jump to content

Fried plantain (Abinci)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fried plantain
dish (en) Fassara da abinci
Kayan haɗi cooking banana (en) Fassara
plantain (en) Fassara
Said to be the same as (en) Fassara Alloco (en) Fassara
kelewele
Kelewele

Kelewele abinci ne na al’ada da ake yinsa a ƙasar Ghana, wanda ake yi da ayaba mai ɗan tsami da aka yanka a soya tare da kayan kamshi.[1] Yana da ɗanɗano mai daɗi, kuma ana yawan amfani da shi wajen cin abincin dare ko kuma kayan ciye-ciye.[2]

Kayan Amfani Wajen yin Kelewele

[gyara sashe | gyara masomin]

Kelewele ana yin sa ne da sinadarai wadanda suka haɗa da:

  • Ayaba (Plantain) Ayaba mai ɗan tsami wadda ba ta cika nuna sosai ba.[3]
  • Tafarnuwa Ana murza tafarnuwa don ƙara ɗanɗano.
  • Barkono Barkono mai ɗan yaji don ya ba kelewele ɗanɗano mai zafi.
  • Citta Ana amfani da ginger don ya ƙara ƙamshi da ɗanɗano.
  • Gishiri A kan ƙara gishiri domin karin ɗanɗano.

Yadda ake yin Kelewele

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Ayaba Ana yanka ayaba ta yanda zata yi ƙanana kuma kaɗan siriri.
  • Kayan Kamshi A hade tafarnuwa, ginger, barkono, da gishiri a murza su wuri daya.
  • Jiƙa Ayaba da Kayan Kamshi A jiƙa yankakken ayaba a cikin kayan kamshi a barshi na wani ɗan lokaci don ya sha.
  • Soyawa A soya ayabar cikin mai mai zafi har sai ta yi launin zinariya ta yi kauri.

Muhimmanci Kelewele a Kasar Ghana

[gyara sashe | gyara masomin]

Kelewele abinci ne da ke bayyana al’adun dake kasar Ghana, kuma ana yawan cin shi a lokutan hutu ko bukukuwa. Ya shahara wajen kayan ciye-ciyen dare musamman a biranen Accra da Kumasi, inda ake siyar da shi a titunan gari. Kelewele yana dauke da carbohydrates daga ayaba, sannan yana da wasu sinadarai daga ginger da tafarnuwa wadanda ke taimakawa wajen inganta garkuwar jiki.