Gandun Dabbobi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gandun Dabbobi
Asali
Mawallafi George Orwell (en) Fassara
Shekarar ƙirƙira 1945
Asalin suna Animal Farm
Ƙasar asali Ingila
Bugawa Harvill Secker (en) Fassara
Shafuka 92
Distribution format (en) Fassara hardback (en) Fassara da paperback (en) Fassara
Characteristics
Genre (en) Fassara roman à clef (en) Fassara, satirical fiction (en) Fassara, fable (en) Fassara da dystopian fiction (en) Fassara
Harshe Turanci
Kintato
Narrative location (en) Fassara Ingila da Manor Farm (en) Fassara
Muhimmin darasi totalitarianism (en) Fassara
Tarihi
Chronology (en) Fassara

Coming Up for Air (en) Fassara Gandun Dabbobi Nineteen Eighty-Four (en) Fassara

Gandun Dabbobi na Bala A. Funtua fassarar shahararren littafin nan ne mai suna Animal Farm, wallafar wani baturen Ingila wanda ake kira George Orwel, ko da yake dai sunansa na gaskiya shi ne Eric Blair. Gandun Dabbobi dai shagube ne, waton gugar zana akan juyin mulkin da akayi a ƙasar Rasha, a shekarar 1917 – wanda akayi amfani da dabbobin da ake kiwo a gandu domin isar da sako. Wannan littafi ne mai manufar jigon ilmantarwa, nishadantarwa da wayar da kai ta hanyar zambo da kuma farfaganda. Gandun dabbobi littafine mai dauke da hikima da hangen nesa.

Labarin Littafi[gyara sashe | gyara masomin]

Wadannan dabbobi sune suka taru a karkashin wani tsohon alade waishi Dattijo (Old Major) , don yayi musu bayani na wani irin mafarki da yayi, da kuma yanda zasu kori Nomau (Mr. Jones) daga gonarsa don ta zama tasu. Daga karshe dai sunci nasara wajen korar Nomau daga gandu ta hanyar tawaye (revolution) , kuma gandu ya koma nasu, ya zama sune wuka sune nama, bayan mutuwar Dattijo, wanda ya mutu kwana ukku bayan jawabinsa.

Kokarin marubucin[gyara sashe | gyara masomin]

Marubucin yayi amfani da aladu a matsayin dabbobi masu kaifin tunani kuma masu iya tafiyar da ragamar mulkin gandu, Musamman Dantulu (Snowball) , Maitumbi (Napoleon) , da Karambana (Squealer) – Sauran dabbobi sun hada da su Aura (Benjamin) , Akawal (Boxer), Godi (Clover), Hoge (Minimus), Kyalla (Muriel) , Sangartatta (Mollie) Barde (Pinkeye) , Burtu (Moses), Dafale (Bluebell), Durwa (Jessie), ‘Yarbaka (Pitcher) da dai sauransu. Dabbobin gandu dai sunci nasarar tawaye ne da Karin karfin gwuiwar Wakar Dabbobin Rugu wadda ke dumamasu :

Dabbobin rugu duk ku saurareni Dabbobin ko ina ku saurareni, Nazo da zance mai faranta rai Nan gaba ba wuya, idan mun niyya Lalle muna iya ture Dan Adam. Daga nan sai kasa ta zanto tamu Mune muke iko da ko ina… Shafi name 9 Sunan gandu ya canza daga Gandun Nomau zuwa Gandun Dabbobi, har sun tsara dokokinsu wadanda zasu yi amfani dasu. Ga alamu dai, Dantulu shugaba ne nagari mai hazaka da son ci gaban dabbobi – ‘‘Ya ‘yan’uwana, mu nufi saura, mu maida himmar yankan tattaka, mu ga munfi Nomau da barorinsa maida hankali Shafi na 18.

An fara samun banbancin zaman gandu, da nuna fifiko da son kai tun lokacin da aka fara tatsar madara ana mallakawa aladu kawai, harda nunannen mangwaro ma sai aladu kawai ke moriyarsa. A duk lokacin da sauran dabbobi suka fara guna-guni, sai a tura musu Karambana don yayi musu bayani. Saboda baiwarsa ta iya magana, Karambana zai iya canza baki zuwa fari. Yakan ce: Ya ‘yan’uwana, ina fatar zaku lura fa da cewar mu aladu, ba muna yin haka ne don nuna fifiko ko son kai. Da yawa daga cikinmu ba mu son madara ko mangwaro. Ni kaina bani kaunarsu. Dalilin da yassa kawai muke shansu shine don mu tsare lafiyarmu. Madara da mangwaro, Ya yan uwana, ilimin kimiya ya tabbatar da amfaninsu ga aladu. Mu aladu, masu aikin tunani ne kawai, dukkan shirye-shirye da sarrafar da aikin gandun nan ya dogara ne fa a kanmu. Dare da rana fa tsaye muke don jin dadin ku kawai. Saboda ku ne muke shan madara da mangwaron nan. Shin me kuke zato idan muka kasa yin aikinmu yadda ya kamata? Nomau sai ya dawo… cikinmu babu wanda yake son yaga Nomau ya dawo. Shafi na 26. Hassada da babakeren Maitumbi sunsa yayi kulla-kullar korar Dantulu a gandu, saboda babu jituwa a tsakaninsu, duk lokacin da daya yacce wannan ‘fari’ ne sai dayan yace a’a, ‘baki’ ne. Haka sunka saba yi har anka iso ga muhawarar ginin famfo (windmill) . Jim kadan da korar Dantulu, sai ga aladu sun fara karya dokokin gandu: Duk abu mai kafa biyu abokin gaba ne Duk abu mai kafa hudu, ko fuffuke, dan’uwanmu ne Kada dabbar da ta kuskura ta sa tufafi Kada dabbar da ta kushura ta kwanta kan gado [da barguna] Kada dabbar da ta kuskura ta sha giya [har ta bugu] Kada dabbar da ta kuskura ta kashe ‘yar’uwarta [babu dalili] Duk dabbobi darajarsu daya [amma wasu sun dara wasu] Dabbobi sun koma da cewa mulkin Nomau yafi mulkin aladu dadi, ba wa

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]