Gasar Cin Kofin Kwallon Kwando ta Mata ta Tunisiya ko a cikin ( yaren Larabci: كأس تونس لكرة السلة للسيدات) gasar ƙwallon kwando ce ta mata a Tunisiya. An kirkiro gasar ne a shekarar 1966 da Hukumar Kwallon Kwando ta Tunusiya ta mulki da kuma gudanar da ita, kuma tun ana gudanar da ita kowace shekara. Kulob din da ke da rinjaye shi ne Zitouna Sports daga Tunis mai jumullar kofuna 13 a matsayin tarihin Stade Tunisien Shima daga Tunis mai Kofuna 9, sai matsayi na uku CS Sfaxien daga Sfax mai kofuna 7. [1]