Gidan Kayan Tarihi Na Wajir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gidan Kayan Tarihi Na Wajir
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaKenya
County of Kenya (en) FassaraWajir County (en) Fassara
BirniWajir (en) Fassara
Coordinates 1°44′49″N 40°03′52″E / 1.74696553°N 40.06451312°E / 1.74696553; 40.06451312
Map
Contact
Address P3W7+QRJ Wajir, Kenya
Gidan tarihi
Tabari gidan tarihin wajir na kenya

Gidan kayan tarihi na Wajir (Swahi; Somali) wani gidan tarihi ne dake arewa maso gabashin Kenya. Gidan kayan tarihi ne ke kula da nuna al'adu daban-daban da ke zaune a Wajeer. Gidan adana kayan tarihi na Hukumar Kula da Gidajen tarihi ta Kenya mallakar gwamnati ne ke kula da gidan kayan gargajiyan. Wannan shine gidan tarihi na farko a gundumar Wajeer. [1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Ginin da gidan kayan tarihi yake na daya daga cikin mafi dadewa a Wajeer, fursunonin yakin Italiya ne suka gina wannan ginin. [2] A cikin shekarar 2007, Hukumar Gidajen tarihi ta Kenya ta gudanar da wani bincike inda ta ba da shawarar kafa gidan tarihi a babbar gundumar Wajeer.[3] An mayar da ginin zuwa gidan kayan gargajiya kuma an kaddamar da shi a cikin shekarar 2011. [4] Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa aka samar da gidan tarihin shine don ƙarfafa yawon shakatawa a Arewacin Kenya.[5] Bude gidan tarihin ya samu halartar karamin ministan raya arewacin Kenya Mohammed Ibrahim Elmi. Ƙungiyar Gidan Tarihi ta Kenya ta ba da kyautar na'urar DVD, tsarin wutar lantarki da na'urar TV ga gidan kayan gargajiya.[6] A watan Disambar 2015, an gudanar da bikin al'adu na Wajeer karo na biyu a gidan kayan gargajiya, gidan adana kayan tarihi na kasar Kenya da gwamnatin gundumar Wajeer ne suka shirya taron.[7]

Collections (Tari)[gyara sashe | gyara masomin]

Gidan kayan tarihin yana adana abubuwan tarihi da na halitta na wannan yanki na Kenya.[8] Gidan kayan tarihin ya ƙunshi abubuwan baje koli ga al'ummomin Arewacin Kenya kamar su Samburu, Gabra, Daasanach, El Molo, Boorana, Somaliya, Pokot, Turkana da Rendile.[9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Wajir Country Integrated Development Plan 2018-2022" (PDF). Ministry of Devolution. 2020. Retrieved 2021-12-15.
  2. Muchui, David (2020-07-02). "Tour Wajir for a feel of WWII, cultural heritage" . Nation . Retrieved 2021-12-16.
  3. "Wajir Museum Opening" (PDF). Kenya Museum Society. 2013. Retrieved 2021-12-15.
  4. Silverman, Raymond; Abungu, George; Probst, Peter (2021-08-30). National Museums in Africa: Identity, History and Politics . Routledge. ISBN 978-1-000-42864-3
  5. "Wajir Museum: Geographical location and historical background" (PDF). Wajir Live . 2012. Retrieved 2021-12-15.
  6. Mbuthia, David (2013). "New museum spotlights region with ambitions for tourism" (PDF). Kenya Museum Society . Retrieved 2021-12-15.
  7. "National Museums of Kenya 2015-2016 Annual Report" (PDF). National Museums of Kenya. Retrieved 2021-12-21.
  8. Olubayi, Christine (2019-08-05). "The undiscovered side of Wajir" . KBC. Retrieved 2021-12-16.
  9. "Museo Wajir" . Casa África (in Spanish). 2019-04-29. Retrieved 2021-12-16.