Gidan Korau (Masarautar Katsina)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Shi Gidan Korau da ke Katsina, Korau ɗin ne ya gina shi a wajen farko-farkon ƙarni na goma sha biyar. Korau an ce Musulmi ne wanda ake yi masa laƙabin Muhammadu Korau. Ya fito ne daga ƙabilar Wangarawa da ke rusasshiyar daular Mali. Shi Korau, tare da jama’arsa, sun mamaye ƙasar ‘Yandoto, wadda ke Zamfara, a farkon ƙarni na goma sha biyar (15). Daga nan kuma suka gangaro Katsina-Jigawa, suka yaƙi Sarkin Katsina da ke birnin Katsina mai suna Jibda Yaƙi Sanau.

Tsohon garin Katsina a shekarar 1911
Gidan adana Tarihin a Katsina

Bayan cin nasara yaƙi, sai Korau ya ɗare karagar mulkin Katsina ya zama Sarkin Katsina na farko a tsatson Wangarawa. Kamar yadda bayani ya gabata cewa, Korau ne ya gina gidan Sarkin Katsina na yanzu da ke Cikin Gida, ya zauna a ciki har ƙarshen rayuwarsa. Haka ‘ya’ya da jikoki waɗanda suka yi Sarautar Katsina a daular Wangarawa, su ma a nan suka zauna tun daga shi Korau wanda ya yi zamani daga 1348-1398, har dai a ƙarshen mulkin Wangarawa a shekara ta 1807. An yi Sarakunan Katsina na Wangarawa waken guda ashirin da tara, kuma duk a nan Gidan Korau wanda ke Cikin Gida, suka yi Sarauta.

Muhimmai daga cikin waɗannan Sarakuna na Haɓe zuriyar Wangarawa, da suka yi mulkin Katsina, daga nan Gidan Korau da ke Cikin Gida, akwai Korau shi kansa. Akwai Ali Murabit, Ali Karyagiwa, Ibrahim Maje, Uban Yara, Janhazo, Gunawa Agwaragi, Sarki Gozo, Bawa Ɗangiwa, Maremawa, Magaji Halidu, da sauransu.

A lokacin mulkin Korau (1348-1398) aka gina gidan Sarkin Katsina da ke Cikin Gida, a lokacinsa ne aka tabbatar da kafuwar ƙasar Katsina wadda ta haɗa da Karofi, ‘Yanɗaka Durɓi, da sauran su, mai babban birni a Katsina, mai fada a Cikin Gida. Ali Murabit (1452-1475) da ya biyo baya, shi ya sa aka gina ganuwar Ƙofar Soro, wadda ta zagaye Gidan Korau, wadda aka yi wa ƙofofi guda biyu, Ƙofar Soro ta shiga fadar Sarki, da Ƙofar Bai, ta bayan gidan Sarki.

Tun daga zamanin Ali Murabit ne aka fara samun kafuwar Cikin Gida. Daga baya kuma, Ali Murabit, ya fara gina babbar ganuwar Katsina, wadda ta zagaye duk unguwannin da ke cikin birni Katsina. Amma ba a ƙarasa ginin ba sai zamanin Ibrahim Maje (1599-1613). Shi Ibrahim Maje baya ga ci gaba da ginin ganuwa, ya kuma ƙarfafa addinin Musulinci a ƙasar Katsina baki ɗayanta.

Shi kuma Ali Karyagiwa (1475-1525) wanda ya yi mulki kafin Ibrahim Maje, ya ƙara faɗaɗa ƙasar Katsina, inda aka kai yaƙi har Kuyambana da Birnin Gwari da Zamfara, don ƙara samun ƙasar mulki. Umurnin yin hakan ya fito ne daga fadar Cikin Gida. Kuma a zamanin Karyagiwa aka karɓi baƙuncin wani malami mai suna Muhammad Bin Ahmad Al-Tszakht, wanda aka fi sani da Ɗantakun. Shi Ɗantakun, ya zama babban alƙali a Katsina.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

1. Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria. 2. Kangiwa M.M. (2014). A short Historical Guide on Katsina National Monuments and Sites.