Gidan Tarihin Gargajiya na Melitopol

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
hoton kayan tarihin
hoton gidan tarihi
hoton gidan tarihi

 

Gidan Tarihin Gargajiya na Melitopol
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaUkraniya
Oblast of Ukraine (en) FassaraZaporizhzhia Oblast (en) Fassara
City of regional significance of Ukraine (en) FassaraMelitopol (en) Fassara
Coordinates 46°50′43″N 35°22′53″E / 46.845278°N 35.381389°E / 46.845278; 35.381389
Map
History and use
Opening1921
Contact
Address вулиця Михайла Грушевського, 18, Мелітополь, Запорізька область, Україна
Offical website

Gidan Tarihin Gargajiya ba Melitopol Museum ( harshen Ukraiine : Мелітопольський краєзнавчий музей ) gidan kayan gargajiya ne da ke Melitopol, Ukraine.[1] Yana nuna abubuwan da suka shafi tarihi da yanayin na asali na yankin. Gidan kayan gargajiya lr yana cikin tsohon gidan Chernikov, wanda aka gina a shekara ta alif dari tara da goma sha uku 1913. Darektan gidan tarihin ya zuwa shekara ta 2022 darektan ta Leila Ibragimova .

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Tattara kayan tarihi a gidan ya fara ne a cikin shekara ta alif dari tara 1900, lokacin da Melitopol Zemstvo ya sayi tarin tsuntsayen taxidermied wanda yakai kimanin guda dari da tamanin 180 akan kudi 750 rubles . A cikin shekara ta alif dari tara da goma 1910, an haɗa tarin Zemstvo tare da tarin Melitopol Real School . A ranar 1 ga watan Mayun shekara ta alif dari tara da ashirin da daya 1921, an bude gidan kayan tarihi na yankin Melitopol a wani gini da ke kan titin Dzerzhinsky sannan darektansa na farko shine mai koyarwa D. Serdyukov.[2]

Ginin Gidan[gyara sashe | gyara masomin]

An gina ginin bene mai hawa uku na ɗan kasuwa Ivan Chernikov na Second Guild a shekara ta 1913. An ƙawata cikin ginin sosai da stucco na fasaha. [3] an zabi Ivan Egorovich Chernikov a matsayin shugaban Melitopol City Council har sau biyu- daga 1891 zuwa 1895, sannan kuma daga 1901 zuwa 1905. ’Yan’uwan Chernikov sun mallaki gidan kasuwanci da ya ƙware wajen samar da masana’antun Melitopol. A bene na farko na gidan Chernikov akwai wani kantin sayar da injunan dinki na kamfanin Amurka " Singer ", kuma benaye biyu na sama na gidan sun kasance wuraren zama.[4]

A cikin shekara ta 1917, iyalan Chernikov sunyi kaura zuwa Faransa. Daga watan Yuni zuwa Oktoban 1920, ginin ya kasance hedkwatar Janar Wrangel . A cikin shekarun 1920s da 1930s, ginin ya kasance gida ga kungiyoyin motsa jini. A lokacin yakin duniya na biyu, gidan ya kasance ofishin kwamandan Jamus, kuma bayan 'yantar da Melitopol ya kasance ofishin kwamitocin jam'iyyar gurguzu da na Komsomol . A cikin benen ginin na kasa akwai bankin ajiya wanda ya wanzu har tsawon shekaru da yawa. A cikin shekara ta 1967 hukumomin birnin sun mayar da ginin zuwa gidan kayan tarihi na tarihin gida.[5]

Kayan da aka ajiye[gyara sashe | gyara masomin]

Kayayyakin da ke gidan tarihi na Melitopol na Tarihin Gida ya ƙunshi abubuwa kusan guda 60,000. Ya ƙunshi tarin gwal-gwalan Scythian na musamman daga karni na huɗu BC, wanda aka samu a sakamakon tono Melitopol kurgan. Gidan kayan gargajiya yana da tarin kaya masu yawa, wanda ya haɗa da tsabar kudi, umarni da lambobin yabo, alamu, hatimi, bajoji da takardun banki. An samu yawancin tarin kayan ne a shekarar 1986 sakamakon tsintuwar tsabar azurfa na bazata da akayi a tsakanin 1895-1925. Tarin kayan yaduka yana nuna abubuwan ban mamaki na gundumomi daban-daban na Melitopol. Tarin zane-zane na kayan ado ya haɗa da kayan kayan ado na gargajiya, porcelain da kuma tukwane. Tarin kayayyaki na zahiri sun haɗa da ƙirar ƙasa, ilmin burbushin halittu, nazarin halittu, dabbobi da samfuran halitta.[6]

Gallery[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Melitopol". www.encyclopediaofukraine.com. Retrieved 2022-03-10.
  2. "Просвіта"". 2013-10-29. Archived from the original on 29 October 2013. Retrieved 2022-03-10.
  3. Chukhraenko AA Stucco decorations of the building of the Museum of Local Lore // Melitopol Journal of Local Lore, 2018, №13, pp. 75-80 (in Russian).
  4. "Мелитопольский городской краеведческий музей - MGK Мелитополь". www.mgk.zp.ua. Retrieved 2022-03-10
  5. Страница не найдена (404-я ошибка) / Мелитопольский краеведческий музей / Музейний простір. Музеї України та світу". prostir.museum. Retrieved 2022-03-10.
  6. "Doukhobor Memorial Stone from the Village of Bogdanovka". Doukhobor Heritage. 2020-01-25. Retrieved 2022-03-10.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]