Gidauniyar Dasa itatuwan 'ya'yan itace

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gidauniyar Dasa itatuwan 'ya'yan itace
Bayanai
Iri nonprofit organization (en) Fassara
Ƙasa Tarayyar Amurka
Mulki
Hedkwata Pittsburgh (en) Fassara
Tsari a hukumance 501(c)(3) organization (en) Fassara

ftpf.org


Gidauniyar Dasa itatuwan 'ya'yan itace (FTPF) ƙungiya ce mai zaman kanta ta Pittsburgh tareda reshe a babban tsibirin Hawaii da shirye-shiryen agaji a duniya. FTPF wata ƙungiya ce mai zaman kanta ta ƙasa da ƙasa da ta keɓe don dasa itatuwan 'ya'yan itace don rage yunwar duniya, yaƙi da sauyin yanayi, ƙarfafa al'ummomi, da haɓɓaka iska, ƙasa, da ruwa dake kewaye. Shirye-shiryen FTPF suna bada gudummawar gonakin noma da dabarun girbi inda girbin zaifi yiwa al'ummomi hidima ga tsararraki, a wurare kamar makarantun jama'a, wuraren shaƙatawa na birni,lambunan al'umma, unguwannin masu ƙaramin ƙarfi, ajiyar 'yan asalin Amurkawa, wuraren bada agajin yunwa na duniya, da wuraren kare dabbobi. Manufar FTPF ta musamman tana amfanar muhalli, lafiyar ɗan adam, da jin daɗin dabbobi—duk lokaci guda. David (Avocado) Wolfe ne ya kafa FTPF. Mai hangen nesa na FTPF da shugaban kasa, David Wolfe, da mahaliccinsa da TreeEO, Cem Akin, suna tunanin duniya mai lafiya inda itatuwan 'ya'yan itace ke bada yanayin muhalli tareda iska mai kyau, ƙasa mai wadata, da abinci mai ɗorewa.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]