Hari a Ofishin Yaɗa Labarai na Jihar Enugu, 2014
Hari a Ofishin yaɗa labarai a Jihar Enugu, 2014 | ||||
---|---|---|---|---|
attack (en) | ||||
Bayanai | ||||
Kwanan wata | 5 ga Yuni, 2014 | |||
Perpetrator (en) | Biafra Zionist Front | |||
Wuri | ||||
|
An kai harin ne a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2014 a jihar Enugu, inda kimanin ƴan kungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra Biafra Zionist Federation, su 13 suka kai wa ofishin yaɗa labarai na jihar Enugu (ESBS) hari a ƙoƙarin da suke na sanar da jama’a a gidajen rediyo da talbijin na ayyana ƴanncin kai na ƙasar Biafra.[1][2]
Wai-wa-ye
[gyara sashe | gyara masomin]Tun bayan rashin nasarar Biafra a ƙarshen yakin basasar Najeriya, ana ta samun tarzoma a wasu lokuta a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Ƙungiyar fafutukar neman kafa ƙasar Biafra (BZF) da kungiyar fafutukar tabbatar da kafa kasar Biafra (MASSOB) sun kasance mafi farin jini a yankin.
Martani
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu jami’an ESBS ne suka sanar da rundunar ƴan sandan Najeriya cikin gaggawa a isar ‘yan bindigar. Nan take NPF ta mayar da martani inda ta kashe wani dan ƙungiyar tare da kame sauran a wani harbe-harbe da aka shafe sa’oi da dama ana yi. Shugaban tawagar sojojin Najeriya ya samu rauni sosai a lokacin da lamarin ya faru.[3][4]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Tony Edike (2014-06-06). "Pro-Biafra Group bid to seize Enugu Radio and TV station foiled". vanguardngr.com. Retrieved 11 July 2014.
- ↑ "BZF attempts to seize Enugu Radio Station". akpraise.com. Archived from the original on 15 July 2014. Retrieved 11 July 2014.
- ↑ Emmanual Uzordinma (5 July 2014). "Biafra Group attempt to seize Enugu Radio, TV station. Kills Police officer". dailypost.ng. Retrieved 11 July 2014.
- ↑ IHUOMA CHIEDOZIE (5 July 2014). "Two Killed in an attempt to declare Biafra in Enugu". punchng.com. Archived from the original on 6 June 2014. Retrieved 11 July 2014.