Jump to content

Hari a gidan gwamnatin Enugu, 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHari a gidan gwamnatin Enugu, 2014
Iri attempted coup d'état (en) Fassara
Kwanan watan 8 ga Maris, 2014
Wuri Enugu State House of Assembly (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Tutar Enugu

An kai harin gidan gwamnatin Enugu na shekarar 2014 ne a ranar 8 ga watan Maris din shekarar 2014, lokacin da ƴan ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra Zionist Federation suka mamaye gidan gwamnatin na tsawon sa’o’i 4, suka kafa tutar ƙasar Biafra a kofar gidan.[1] Shugaban ƙungiyar Barista Benjamin Onwuka ya bai wa ƴan Najeriya mazauna yankin Biafra wa’adin barin ƙasar kafin ranar 31 ga watan Maris, 2014 ko kuma su fuskanci zubar da jinin da zai biyo baya.[2]

Da farko dai an ruwaito cewa wata ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra ta MASSOB ce ta kai harin, amma daga baya an yi watsi da wannan bayanin bayan da BZF ta ɗauki alhakin kai harin.[3] Rundunar ƴan sandan najeriya ta kama Benjamin Onwuka bayan yunƙurin kai makamancin wannan hari a gidan rediyon jihar Enugu.[4]

Duba sauran wasu abubuwan

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Why we attacked Government House - Pro Biafran Group". sunewsonline.com. Retrieved 11 July 2014.
  2. "We seized Government house for 4 hours - Onwuka". vanguardngr.com. Retrieved 11 July 2014.
  3. "MASSOB behind Government House attack". pointblanknews.com. Retrieved 11 July 2014.
  4. "Security Beefed up in Enugu Government House over Fear of fresh attacks". dailyindependentnig.com. Archived from the original on 14 July 2014. Retrieved 11 July 2014.