Harin Bom a Mubi, 2017
Appearance
|
attempted murder (en) | ||||
| Bayanai | ||||
| Kwanan wata | 2017 | |||
| Wuri | ||||
| ||||
A ranar 21 ga watan Nuwamban 2017, an kai harin ƙuna baƙin wake a garin Mubi da ke jihar Adamawa a Najeriya. [1] Wani matashi ya tayar da bam din a cikin wani masallaci a lokacin da masu ibada suka isa Masallacin domin gudanar da sallar asuba a babban garin da ke gabashin Najeriya, inda suka kashe mutane 50. [1]
Alhakin kai harin
[gyara sashe | gyara masomin]Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin. Babbar ƙungiyar Boko Haram ta fara tayar da kayar baya a shekarar 2009. Sune ke kai mafi yawan hare-haren da ke afkuwa a Najeriya tun a wancan lokaci. Ana zarginsu da kai harin bam, da kuma hare-haren da aka kai a Mubi a 2012, 2014 da 2018.
