Harrison Kombe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harrison Kombe
Member of the National Assembly (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1956 (67/68 shekaru)
ƙasa Kenya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Malami da university teacher (en) Fassara

Harrison Mwalimu Garama Kombe (an haife shi a shekara ta 1956 a Magarini, gundumar Kilifi) malami ne kuma ɗan siyasa ɗan ƙasar Kenya. An fara zaɓar sa ne a majalisar dokokin Kenya daga mazaɓar Magarini a kan tikitin jam’iyyar Shirikisho a shekarar 2002. Ya sha kaye a shekarar 2007 kuma ya koma majalisar a shekarar 2013 aka sake zaɓen shi a shekarar 2017 kafin a sake kayar da shi a zaɓen shekara ta 2022 na majalisar.[1]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

An horar da Harrison Kombe a Makarantar Fasaha ta Machakos. A shekarar 1979 ya shiga Lawfords Hotel a matsayin ma'aikacin lantarki. Daga shekarun 1985 zuwa 1986 ya kasance malami a makarantar fasaha ta Nairobi sannan ya koma makarantar sakandare ta Malindi inda ya koyar daga shekarun 1987 zuwa 1988.[2] Ya koma Kinango Secondary and Technical School kuma ya koyar a can na tsawon shekara ɗaya kafin ya wuce Sheikh Khalifa Secondary & Technical School inda ya karantar daga shekarun 1990 zuwa 1996. Ya kare aikinsa na koyarwa a Makarantar Sakandare ta Marafa da Sakandaren Kikoneni a shekarar 2002 lokacin da ya shiga harkokin siyasa.[3]

An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokokin Kenya na 9 daga mazabar Magarini akan tikitin jam'iyyar Shirikisho a shekarar 2002. Ya sha kaye a zaɓen 2007 ta hannun Amason Kingi Jeffah. Ya kalubalanci sakamakon a kotu wanda ya kai ga soke zaɓen kuma aka ba da umarnin gudanar da zaɓen fidda gwani. A zaɓen fidda gwani, Amason Kingi Jeffah ya sake kayar da shi. Bayan ya sha kaye, ya koma aikin koyarwa kuma ya koyar daga shekarun 2008 zuwa 2013 lokacin da ya kwato kujerar Magarini a majalisar dokoki kan tikitin jam'iyyar URP da goyon bayan kawancen Jubilee. A zaɓen 2013, Amason kingi jeffa mai ci bai tsaya takara ba yayin da ya tsaya takara kuma ya lashe kujerar gwamna a Kilifi. A majalisa ta 11, Kombe ya yi aiki a kwamitin kula da abinci da kiwon lafiya da kuma kwamitin sashen ilimi, bincike da fasaha. An sake zaɓen shi a shekarun 2017 da 2022 amma zaɓen 2022 ya kalubalanci abokin hamayyarsa wanda ya kai ga soke zaɓen da manyan kotuna da kotun ɗaukaka kara suka yi bisa dalilan rashin bin ka’ida.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Magarini MP Harrison Kombe bites the dust after court nullifies his election". Nation (in Turanci). 2023-03-03. Retrieved 2023-11-17.
  2. Kithi, Marion. "High Court nullifies Magarini MP Harrison Kombe's election". The Standard (in Turanci). Retrieved 2023-11-17.
  3. "Kombe wins round one as Apex court suspends decision nullifying his election". The Star (in Turanci). Retrieved 2023-11-17.
  4. Kithi, Marion. "High Court nullifies Magarini MP Harrison Kombe's election". The Standard (in Turanci). Retrieved 2023-11-17.