Jump to content

Nasiru Sule Garo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Hon Nasiru Sule Garo)
Nasiru Sule Garo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: Gwarzo/Kabo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015
District: Gwarzo/Kabo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Gwarzo/Kabo
Rayuwa
Haihuwa 28 ga Janairu, 1974 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
New Nigeria People's Party

Nasiru Sule Garo (an haife shi 28 ga Janairu 1974) shi ne kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Najeriya. ya kasance dan majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya.[1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nasiru Sule Garo a Garin Garo Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano, Najeriya a ranar 28 ga Janairun 1974. Ya halarci makarantar firamare ta Garo Central, da karamar sakandare garo, da Kwalejin fasaha ta Bagauda kafin ya wuce Jami'ar Bayero Kano inda ya samu Diploma a Mass Communication, Advance Diploma information management da B-Sc a fannin kimiyyar siyasa. Nasiru ya auri Fatima L Sule kuma Allah ya albarkace su da haihuwa.

Nasiru ya yi aiki da Garo Tannery and Trends Venerate ltd, duk a Kano, Ya kuma yi mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano daga 2002 zuwa 2003. An zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). An zabi Nasiru a matsayin dan majalisar wakilai a shekarar 2011 a jam'iyyar PDP sannan kuma a shekarar 2015 a jam'iyyar APC (All People's Congress). Nasiru ya zama kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Najeriya a watan Yunin 2023.

  1. "Hon. Nasiru Sule Garo". Nigerian House of Representatives.