Honda Insight

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Honda Insight
automobile model (en) Fassara
Bayanai
Manufacturer (en) Fassara Honda (en) Fassara
Brand (en) Fassara Honda (en) Fassara


Honda_Insight_Concept_004
Honda_Insight_Concept_004
2001_Honda_Insight_Hybrid_1.0i_(Rear)
2001_Honda_Insight_Hybrid_1.0i_(Rear)
Honda_Insight_IMA
Honda_Insight_IMA
2019_Honda_Insight_LX,_1.4.20
2019_Honda_Insight_LX,_1.4.20
Honda_Insight_1
Honda_Insight_1

Honda Insight wata hadaddiyar mota ce ta lantarki da Kuma man fetur wacce kamfanin Honda ta kera kuma take saida wa. Ƙirar ta ta farko ta kasance mai kofa biyu, wurin fasinja biyu a baya (1999-2006) kuma a ƙirarta ta biyu taa kasance mai kofofi huɗu, mai ɗaukar fasinja biyar (2009-2014). A cikin ƙirar ta ta uku, ta zama sedan mai kofa huɗu (2018-2022). Ita ce samfurin farko na Honda tare da Integrated Motor Assist System da kuma mafi kyawun man fetur da ake samu a Amurka ba tare da toshewar inji ba - na tsawon lokacin aikinta.

Honda ya gabatar da Insight na ƙarni na biyu a Japan a cikin Fabrairun shekarar 2009 da kuma a Amurka a shekaran Maris 24, 2009. Insight ta kasance mafi ƙarancin tsadar mota a Amurka. A cikin Disamba 2010, Honda ta sake gabatar da samfuri mara tsada daga ƙirar a shekarar 2011. An ƙaddamar da Insight a cikin Afrilu 2009 a Burtaniya a matsayin mafi ƙarancin farashi a kasuwa kuma ta zama mafi kyawun siyarwa ga matasa.

Insight ta zamo motar da aka fi saidawa a kasar Japan a watan Afrilu 2009, a karo na farko ga mota ƙirar hybrid. [1] A cikin watanni goma sha biyu na farko bayan fitowar ta na farko a kasuwannin Japan, an sayar da kirar Insight na biyu guda 143,015 a sassan duniya. A cikin Yuli 2014, Honda ta sanar da ƙarshen samar da Insight da samfurin 2015, tare da motar Honda FCX Clarity mai amfani da man hydrogen da motar lantarki Honda Fit EV.

A wajen taron North American International Auto Show na shekara ta 2018, Honda ta sanar da samfurin Honda Insight na ƙarni na uku, bisa ga tsarin Honda Civic Sedan kira na goma. Ba kamar Insight ɗin da suka gabata ba, sedan ɗin gargajiya ce, ba ɗaga kofa biyar ba. Insight na ƙarni na uku taa ci gaba da siyarwa daga baya waccan shekarar.

A cikin Afrilu 2022, Honda ta ba da sanarwar cewa za a daina Insight bayan shekara ta 2022, yayin da kirar ta zai kare a watan Yuni. An maye gurbinsa da sabon Civic Hybrid.

ƙarni na farko (ZE1; 1999)[gyara sashe | gyara masomin]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Detnews.com | This article is no longer available online | detnews.com | The Detroit News[dead link]