Hussaina Abdullahi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hussaina Abdullahi jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud ta Dan jima a masana'antar tare da yar uwarta Mai suna hassana, tayi fina finai da dama a masana'antar tare da yar uwarta.[1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Hussaina Abdullahi Haifaffiyar Jihar Kano ce a Unguwa uku Karamar hukumar Tarauni an haife ta a ranar 20 ga watan fabrairu shekarar 1995 ita da yar uwarta, ta girma da yar uwarta a cikin garin Kano anan sukai karatu a gaban iyayensu, daga baya suka shigo masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud.

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Hussaina tayi karatun firamare a makarantar unguwa uku special primary school, daga Nan tayi karatun sakandiri a makarantar government girls secondary school Johanna, Bayan ta gama ta shiga kwaleji ta hygiene ta Kano inda tayi difloma ta gama a shekarar 2014.[2]daga nan ta shigo Masana'antar fim ta Hausa kanniwud.

Masana,antar Fim[gyara sashe | gyara masomin]

Hussaina ta shiga masana'antar Kannywood tare da yar uwarta a shekarar 2013 ta hanyar abokin ta wanda darakta ne a masana'antar, ta fara da zuwa kallon yadda ake fim ne daga Nan suka fara fitowa a fim.[3] ta fito a fina finai da dama kuma tafi fito wa tare da yar uwarta.

Aure[gyara sashe | gyara masomin]

Jarumar ba tayi aure ba[4] a halin yanzu bakuma ta taba yin aure ba .

Fina Finan Ta[gyara sashe | gyara masomin]

  • Mairon kauye
  • Juyin Mulki
  • rikita rikita
  • Duk mace mace ce
  • fitsarin fako
  • Ibro Dan karota
  • Hanyar Kano

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.pressreader.com/nigeria/daily-trust-saturday/20160123/281702613727649
  2. https://hausa.legit.ng/1145901-kannywood-yadda-wasu-tagwaye-ke-sharar-fage-a-shirin-fim.html
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
  4. https://www.blueprint.ng/i-wont-wait-for-my-twins-if-i-get-suitor-hassana-musa-abdullahi/