Ibrahim IV na Bornu
Ibrahim IV na Bornu | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a |
Ibrahim IV ya kasance ana yi masa take da Sarkin Musulmi na Kanuri na Bornu daga 1820-1846. Yana daya daga cikin shugabannin da suka gabata daga daular Sefawa.
Rarrabewa akan gaba
[gyara sashe | gyara masomin]Mahaifin Ibrahim, kuma tsohon mai mulkin Bornu, ya yi kira ga El-Kanemi, malamin Islama kuma Jarumi, da ya taimaka ma shi ya yaki Fulani da shugabansu Goni Mukhtar. Su biyun sun sami damar kawar da Fulani daga galibin Bornu. Ayayin gwagwarmayan El-Kanemi ya yi karfi, kuma ya kasance barazana ga gidan sarauta na Sefawa, wanda Ibrahim da mahaifinsa suka kafa, Dunama Daga baya aka kashe Dunama a wani yunkurin kashe El-Kanemi. Dan shi, Ibrahim ya gaje shi. El Kanem kuma akayi rashin sa'a ya mutu a shekara ta 1837, dansa Umar ya gaje shi. Shahararrun sarakunan biyu suna son mamaye madafun iko, har suka dinga yake yake a tsakanin Yan Kanemi da Yan Sefawa. Ibrahim yayi shirin kashe Umar ta hanyar kiran dakaru na waje daga Wadai karkashin umarnin Sarkin Musulmi . Koyaya akayi Umar ya gano shirin, kafin lokacin kuma ya kashe Ibrahim kafin ya gudu daga Bornu. Haka,aka ci gaba da kai hari kan daular Sefawa.