Jump to content

Ibrahim Umaru Chatta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibrahim Umaru Chatta
Rayuwa
Haihuwa 1 Satumba 1958
Mutuwa 19 ga Maris, 2019
Sana'a

Haliru Ibrahim Bologi Umaru Chatta (1 Satumba 1958 - 19 March 2019) ya kasance basaraken gargajiya na farko a Nijeriya na masarautar Patigi kamar Etsu Patigi daga shekarar 1999 zuwa 2001.

Ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati, Illorin daga shekarar 1969 zuwa 1972. Bayan an naɗa masa rawani a matsayin Etsu Patigi a shekarar 1999, ya zama mataimakin shugaban majalisar masarautun jihar Kwara.[1]

An naɗa shi sarauta a matsayin Etsu Patigi tun shekarar 1999 ya kwashe shekaru ashirin akan karagar mulki. Ya gaji Etsu Idirisu Gana, wanda ya yi mulki daga shekarar 1966 zuwa 1996. Dansa Eu Umaru Bologi II ya gaji Chatta.[2]

Chatta ya mutu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a babban asibitin birnin tarayya Abuja.[3]

  1. https://orientmags.com/index.php/2019/03/20/kwara-monarch-etsu-patigi-dies-after-20-years-on-the-throne-saraki-gov-ahmed-governor-elect-others-mourn/[permanent dead link]
  2. https://thenationonlineng.net/kwara-monarch-etsu-patigi-dies-at-65/
  3. https://www.pmnewsnigeria.com/2019/03/23/buhari-eulogises-late-emir-of-patigi/