Igbonla

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Igbonla
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Kasancewa a yanki na lokaci UTC+01:00
Wuri
Map
 8°11′15″N 4°50′04″E / 8.187381°N 4.834553°E / 8.187381; 4.834553

Igbonla Gari ne, a karamar hukumar Irepodun Jihar Kwara, Najeriya, mai kimanin 5.6. km daga Ajasse-Ipo.Garin yana tsakiyar dajin kudancin jihar Kwara. Garin yana karkashin Oba Olabode Jimoh, Eleju na Igbonla. Mutanen garin Igbonla sun shahara da jajircewa da aiki tukuru da neman ilimi. Igbonla gida ne ga fitattun mutane kamar su mai kudin mai da iskar gas, Alh. Yahaya Anifowose, Alhaji Abdulkareem Eniafe, Alhaji Salami Lawal Giwa, Alhaji Ganiyu Oriowo da sauran jama'a.

Al’ummar Igbonla na da dimbin al’umma a sana’ar noma saboda yawan kasan noman da suke dashi.

Har ila yau, al'ummar tana da wuraren hakar ma'adinai inda ake hako albarkatun kasa kamar Tantalite. Igbonla na daya daga cikin mashahurin garin igbomina a jihar Kwara.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]