Ineta Ziemele
Ineta Ziemele (an haife ta ranar 12 ga watan Fabrairu, 1970). masanin shari’a ce ta Latvia kuma alkaliya a Kotun Tsarin Mulki ta Jamhuriyar Latvia tun shekara 2015.[ana buƙatar hujja] A ranar 8 ga Mayu shekara2017 aka zaɓe ta ta zama Shugabar Kotun Tsarin Mulki.
Farkon rayuwa da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Ta kammala karatun digiri daga Faculty of Law na Jami'ar Latvia a shekara1993 kuma ta ci gaba da karatunta a Sweden, inda ta sami digiri na biyu a dokar duniya. Ta ci gaba da samun digiri na uku daga Jami'ar Cambridge a Kwalejin Wolfson.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga Kwamitin Harkokin Waje na Saeima da kuma Firayim Ministan Latvia.
Farfesa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta kuma kasance farfesa a Jami'ar Latvia da Makarantar Shari'a ta Riga. [1]
Alƙalanci
[gyara sashe | gyara masomin]Daga ranar 27 ga Afrilu shekara 2005 zuwa shekara 2015 ta zama alkali a Kotun Turai ta Hakkin Dan Adam. A watan Satumba na shekara2012 ta zama Shugaban Sashe na Hudu na Kotun.