Jump to content

Jabir Sani Mai-hula

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Dr Jabir Sani Mai-hula An haifi Dr Mai-Hula a ranar 3 ga watan Yulin shekara ta alif 1981 a garin Sifawa da ke jihar Sokoto. [1] kwamishinan ma'aikatar lamurran addini ta jihar sokoto 2023 to date

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Jabir Ya Kuma fara karatun addini wajen mahaifi da mahaifiyarsa a gida na Fiƙihun Malikiyya da Iziyya da Ahalari, sannan ya halarci makarantar addini da ke cikin gidansu inda ya karanci Ƙur'ani da Hadisi.

Ya kuma halarci makarantar soro wajen Malam Ibrahim Auro. Ya yi makarantar firamare a Sokoto sai sakandare ta Kwalejin Fasaha ta Rinjin Sokoto.

Bayan nan sai ya samu gurbin yin digiri A Madina a shekarar alif 1999, amma sai da ya fara koyon Larabci na tsawon shekara ɗaya. A lokacin shi ne ɗalibi mafi ƙarancin shekaru Najeriya.

Ya fara karatun digiri a fannin Hadisi a shekarar 2000 inda ya gama a shekarar 2004. Sai ya zarce da karatun share fagen digiri na biyu wato Post Graduate Diploma a Harkokin Siyasa a Musulunci da Alkalanci duk a Madinan inda ya gama shekarar 2005.

Ya koma Najeriya ya yi hidimar ƙasa tsakanin shekarar 2005 zuwa shekarar 2006. Ya fara aikin koyarwa a makaranatr koyon shari'a ta Legal a Sokoto.

A shekarar 2011 ya samu damar zuwa Birtaniya yin digiri na biyu a Jami'ar East London kan Ilimin Musulunci da na Gabas Ta Tsakiya. Ya koma Najeriya a shekarar 2012 inda ya fara aiki a Jami'ar Jihar Sokoto a shekarar 2013.

Ya koma Birtaniya a shekarar 2014 don karatun digirin-dirgir a Jami'ar Nottingham. Ya ka ace Shugaban Musulmin Jami’ar Nottingham (wato Isoc president) daga watan Maris shekarar 2016 zuwa watan Maris shekarar 2017. Ya zama Shugaban sashen Nazarin Larabci da Addinin Musulunci a Jami’ar Jihar Sokoto daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023. Kana an zabeshi Dean Faculty of Arts and Islamic Studies a Maris shekarar 2023. A ranar 27 ga wata July 2023 aka ayyana sunanshi cikin jerin wadanda za a baiwa mukamin kwamishina a Jihar Sokoto. A ranar 23 ga wata August Gwamnan Jihar Sokoto ya rantsar dashi a matsayin Kwamishinan Lamurran Addini na Jihar Sokoto.

Da'awa[gyara sashe | gyara masomin]

Mai-Hula ya fara harkar da'awa tun yana hidimar ƙasa a Abuja a shekarar 2005, yana koyar da mutane karatu da kuma yin wa'azi a Abuja.

A shekarar 2006 ya fara koyar da yaran unguwa a Sakwwato. A shekarar 2009 kuma ya fara babban majalisi a Sokoton.

"Daga lokacin abu ya kankama na sa ɗambar karatun Sinani Abu Daudu har yanzu ana yi ba a kammala ba," in ji shi.

Malam ya ce duk ranakun Alhamis da Juma'a ana karance karance a gidansa.

Ya zama limamin Juma'a sannan akwai masallatan Juma'a uku a Sokoto da ke ƙarƙashinsa.

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Malam Jabir yanada mata biyu da yara biyu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]