Jump to content

Jabir Sani Maihula

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Dr Jabir Sani Maihula,(an haifeshi ranar 3 ga watan Yuni, 1981) a garin Sifawa jihar Sakkwato, Najeriya.[1]

Ya fara karatun firamare a garin Sokoto, bayan gama karatun firare sai ya garzaya makarantar sakandare ta Kwalejin fasaha ta Rinjin, sokoto. Bayan gama sakandare ya samu gurbin yin karatun digiri a birinin Madina a shekarar 1999, shine ɗalibi mafi ƙanƙantar shekaru a cikin abokan karatun shi. Ya sake cigaba da karatun digiri na biyu a jami'ar East London inda ya karanci Ilimin Addinin Musulunci. A shekarar 2013, ya sake komawa Burtaniya yayi digirin-digirgir a jami'ar Nottingham dake kasar Ingila.

Jabir ya fara aiki a makarantar koyon shari'a ta sokoto. Bayan dawowarsa Najeriya yayi aiki da jami'ar Usman dan fodiyo.

  1. "Ku San Malamanku tare da Sheikh Dr Jabir Sani Maihula". BBC Hausa. 26 February 2021. Retrieved 7 December 2024.