Jay Mulucha
Jay Mulucha | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | 20 century | ||||||||||||||||||
ƙasa | Uganda | ||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | basketball player (en) da LGBTQ rights activist (en) | ||||||||||||||||||
|
Jay Mulucha 'yar gwagwarmayar LGBTQI ce daga ƙasar Uganda kuma 'yar wasan ƙwallon kwando ce ta Magic Stormers, ƙungiyar da ke fafatawa a ƙungiyar ƙwallon kwando ta Uganda (FUBA). Jay Mulucha tana ɗaya daga cikin manajojin ƙungiyar.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta fara buga kwallon kwando tun tana matashiya.
Ta kusa mutuwa bayan an kai mata hari a wani gangamin neman 'yancin LGBTQI. A kan gab da kashe kanta, ta kuma yanke shawarar cewa ta tsunduma kanta don yakin neman yancin LGGBTIQ a kasarta ta haihuwa. Ta zama mai kula da Pride Uganda kuma ta halarci bikin Pride na farko a shekara ta, 2012. Ta kuma zama shugabar Fem Alliance Uganda. Fem Alliance ta mai da hankali kan shirye-shiryen horar da kwamfuta da ayyukan karfafa tattalin arziki don samar da karin damammaki ga al'ummar LGBT da ke zaune a Uganda.