João Pedro

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
João Pedro
Rayuwa
Cikakken suna João Pedro Junqueira Jesus
Haihuwa Ribeirão Preto (en) Fassara, 26 Satumba 2001 (22 shekaru)
ƙasa Brazil
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Fluminense F.C. (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Tsayi 1.82 m

João Pedro Junqueira[1] ( an haife shi ranar 26 ga watan Satumba, 2001)[2] ƙwararren dan wasan ƙwallon ƙafan kasar brazil ne wanda ke taka ledarsa a matsayin dan wasan gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta premier league wato Brighton & Hove Albion da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafan kasar tasa ta Brazil.[3]

Rayuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi João Pedro a Ribeirão Preto ga iyayensa Flavia Junqueira da José João de Jesus, wanda aka fi sani da Chicão, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na sannan an daure Chicão na tsawon shekaru goma sha shida a cikin shekarar 2002, wanda yayi takwas, saboda kasancewarsa kayan haɗin kai ga kisan kai.[4][5] A lokacin da aka ɗaure Chicão, shi da Junqueira sun rabu.[6]

Ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 19 ga Agusta a shekarar 2023, an kira Pedro a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil.Pedro zai fara buga wasansa na farko da Brazil a minti na 84 da aka doke su a wasan da suka tashi 1-0 da Morocco.[7] Bayan watanni hudu ne kuma a ranar 6 ga Nuwamba, an kira Pedro zuwa babban tawagar Brazil a karon farko.[8]A ranar 16 ga Nuwamba, Pedro zai fara buga wa Seleção wasa bayan ya zo a matsayin sauye ga Vinícius Júnior da ya ji rauni a minti na 27 a cikin rashin nasara 2-1 da sukayi da kasar Colombia.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]