Jump to content

Johannie Maria Spaan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Johannie Maria Spaan
Rayuwa
ƙasa Afirka ta kudu
Karatu
Makaranta Jami'ar Fasaha ta Tshwane
Jami'ar Pretoria
University of Georgia (en) Fassara
Oregon State University (en) Fassara Doctor of Philosophy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a biologist (en) Fassara

Johannie Maria Spaan 'yar ƙasar Afirka ta Kudu ce masaniya a fannin ilimin halittun daji.

Bayan karatunta a fannin dabbobi da ilimin halittu a Jami'ar Fasaha ta Tshwane, ayyukanta na farko sun kunshi gudanar da nazarin halayya akan squirrels na Cape. Ta kuma yi karatu a Jami'ar Pretoria, kuma ta samu karɓuwa a Kwalejin Kiwon Lafiyar dabbobi, Jami'ar Jihar Oregon da ke kasar Amurka don kammala karatun digiri na uku. Binciken da ta yi ya mayar da hankali ne kan tasirin maganin tsutsotsi a Afirka da kuma tasirinsa ga ɗan Adam.[1] Spaan tana cikin ƴan uwa goma sha biyar waɗanda L'Oréal-UNESCO Awards for Women in Science suka zaɓa don karɓar tallafin karatu na duniya don ci gaba da ayyukan binciken su.[2]

Bayan kammala B.Tech (Tsarin yanayi) a Jami'ar Fasaha ta Tshwane a shekara ta 2005, Spaan ta ci gaba da aikinta na filin Cape Ground Squirrel a matsayin Masaniya a fannin Fasaha na Jami'ar Florida ta Jami'ar Pretoria kuma ta kammala wannan aikin a cikin watan Janairun shekarar 2006.[3] A cikin watan Maris in shekarar 2006 ta koma Entabeni Private Game Reserve a lardin Limpopo na Afirka ta Kudu inda ta yi aiki a matsayin mai bincike da "mai sarrafa gamerange" har zuwa watan Afrilun shekarar 2008. Daga watan Mayun shekarar 2008 zuwa watan Agusta 2012 ta yi aiki a matsayin mataimakiyar mai bincike kan TB Buffalo Project KNP a madadin Jami'ar Jihar Oregon da Jami'ar Jojiya.[4]

A watan Satumba na shekarar 2012 ta shiga cikin shirin PhD na sashen nazarin halittu na Jami'ar Jihar Oregon. Spaan ta kammala karatun digirin digirgir a cikin shekarar 2018 tare da takardar shaidar mai suna Stress Physiology in Free-ranging Female African Buffalo (Syncerus caffer): Environmental Drivers, and Immunological and Infection Consequences.[5]

  1. Johannie Spaan – African Science Heroes". African Science Heroes. 31 March 2012. Retrieved 20 August 2019.
  2. The 14th Annual L'ORÉAL-UNESCO Awards For Women in Science". UNESCO. 28 March 2012. Archived from the original on 2 April 2012. Retrieved 20 August 2019.
  3. Johannie Spaan". LinkedIn. Retrieved 20 August 2019.
  4. Johannie Spaan". LinkedIn. Retrieved 20 August 2019.
  5. Johannie Spaan". LinkedIn. Retrieved 20 August 2019.