John Saka
Appearance
John Saka | |
---|---|
Rayuwa | |
Karatu | |
Makaranta |
University of East Anglia (en) Jami'ar Malawi |
Sana'a | |
Sana'a | chemist (en) |
Employers | Jami'ar Malawi |
Farfesa John Danwell Kalenga Saka shi ne mataimakin shugaban jami'ar Mzuzu na yanzu wanda ya maye gurbin Dr.Robert Ridley wanda ya janye aikinsa a shekarar 2017.[1]
Saka kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jami'ar Malawi wanda ya gaji Farfesa Mkali Idruss Samson Sajidu.[2][3]
An haife shi a Malawi kuma ya yi karatu a Kwalejin Chancellor, Jami'ar Malawi da Jami'ar Gabashin Anglia (PhD, Chemistry).[4] Daga nan ya zama malami a fannin kimiyyar Physical Chemistry a Jami'ar Malawi a shekarar 1986 inda ya zama Farfesa a shekarar 2002. An naɗa shi a matsayin Mataimakin Shugaban Jami'ar Malawi a ranar 2 ga watan Disamba 2013. Shi ne kuma shugaban hukumar shirya jarabawar Malawi.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Mzuzu University has a new Vice Chancellor:Professor John Kalenga Saka". Malawi Nyasa Times-Malawi Breaking News in Malawi. Archived from the original on 2019-05-17.
- ↑ "UNIMA Council Appoints Professor Sajidu as new vice-chancellor". Malawi Nyasa Times-Malawi Breaking News in Malawi. Archived from the original on 2022-03-25.
- ↑ "Prof John Saka is new Vice Chancellor University of Malawi". Malawi Nyasa Times - Malawi breaking news in Malawi. Archived from the original on 2013-11-29.
- ↑ "Professor John Danwell Kalenga Saka". acgt.co.za. Archived from the original on 2017-04-25. Retrieved 2014-01-28.
- ↑ "New board members hired for Malawi National Examinations Board, National Library". Malawi Nyasa Times - Malawi breaking news in Malawi. Archived from the original on 2015-07-30.