Jump to content

Jonathan Deal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jonathan Deal
Rayuwa
Haihuwa 1958 (65/66 shekaru)
ƙasa Afirka ta kudu
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a environmentalist (en) Fassara
Kyaututtuka

Jonathan Deal, masanin muhalli ne na Afirka ta Kudu . An ba shi lambar yabo ta muhalli ta Goldman a shekarar 2013, musamman saboda ƙoƙarin da ya yi na kare yankin Karoo, inda ya jagoranci tawagar masana kimiyya wajen kawo illar muhalli na shirin yin amfani da iskar gas mai yuwuwa a yankin.[1][2][3][4] Jonathan Deal ya kafa Treasure Karoo Action Group a shekarar 2011 kuma ya ci gaba da riƙe muƙamin Shugaba. Ya sami gogewa a wani yunƙuri na ƙasa baki ɗaya yana adawa da Royal Dutch Shell da Sashen Albarkatun Ma'adanai (2010 - yanzu) da nufin daƙile haƙar iskar gas (fracking) a Afirka ta Kudu. Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen kafa ƙungiyar SAFE CITIZEN, ƙungiyar 'yancin walwala da ke mai da hankali kan tsaron 'yan ƙasar Afirka ta Kudu da ke fuskantar dagula ayyukan muggan laifuka a kullum.[5]

Ma'aikacin muhalli na Afirka ta Kudu Jonathan Deal. Ayyukan da ya yi na kare yankin Karoo da tara ƙwararrun masana don gabatar da illolin da aka tsara na haƙar iskar gas a yankin ya ba shi damar samun lambar yabo ta muhalli ta Goldman ta shekarar 2013.[6]

  1. "Prize Recipient, 2013 Africa. Jonathan Deal". Goldman Environmental Prize. Retrieved 7 December 2013.
  2. "Goldman Prize for South African anti-fracking activist Jonathan Deal". africanconservation.org. African Conservation Foundation. 21 April 2013. Archived from the original on 10 August 2022. Retrieved 25 April 2019.
  3. Reddall, Braden (15 April 2013). "South African 'fracktivist' awarded top U.S. environmental prize". in.reuters.com. Reuters. Archived from the original on 25 April 2019. Retrieved 25 April 2019.
  4. Gosling, Melanie (16 April 2013). "Why activist is the real Deal". Cape Times. Retrieved 25 April 2019.
  5. "Jonathan Deal". Safe citizen.
  6. "Jonathan Deal". Edubilla.com (in Turanci). Retrieved 2023-04-15.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]